'Yan Bindiga Sun Mamaye Unguwa a Abuja cikin Dare, Sun Sace Mutane da Dama

'Yan Bindiga Sun Mamaye Unguwa a Abuja cikin Dare, Sun Sace Mutane da Dama

  • Wasu ‘yan bindiga sun kai hari a unguwar Grow Homes da ke Chikakore a Kubwa, babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi garkuwa da mutane da dama
  • Rahotanni sun ce maharan sun shafe kusan awa guda suna addabar al’umma kafin isowar ‘yan sanda, yayin da aka ji musayar wuta mai ƙarfi
  • Al’ummar yankin sun bukaci gwamnati ta gyara hanyar unguwar da kuma kafa ofishin ‘yan sanda domin amsa kiran gaggawa ga irin waɗannan hare-hare

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gungun ‘yan bindiga dauke da makamai sun mamaye unguwar Grow Homes da ke cikin Chikakore, wani yanki na Kubwa a Abuja.

An rawaito cewa maharan sun farmaki mazauna unguwar tare da yin garkuwa da wasu daga cikinsu.

Kara karanta wannan

Makiyaya dauke da makamai sun harbe malamin addini a Makurdi, sun sace mutane 2

Abuja
Yan bindiga sun kai hari Abuja. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton da jaridar Vanguard ta fitar ya nuna cewa harin ya faru ne tsakanin ƙarfe 12:00 na dare zuwa 1:30 na safiyar Litinin, yayin da mutane ke cikin barci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mazaunin unguwar ya ce maharan sun yi nasarar sace wani namiji da mace, amma daga bisani an samu macen a cikin unguwa, inda aka bayyana cewa masu garkuwan sun sake ta.

'Yan bindiga sun mamaye yankin Abuja

Mazaunin unguwar ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun fi karfin rundunar tsaron sa-kai da ke yankin.

Ya bayyana cewa lamarin ne ya ba su damar gudanar da harin ba tare da tangarda ba har zuwa isowar ‘yan sanda.

Mutumin ya ce:

“Sun mamaye unguwar tun ƙarfe 12:00 na dare. Sun shigo da makamai, kuma sun fi ƙarfin ‘yan sa-kai.
"Jami’an ‘yan sanda sun iso wajen ƙarfe 1:00 na dare, inda aka yi musayar wuta na kusan rabin awa,”

Sai dai har yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba, domin wasu daga cikin mazauna yankin na ci gaba da tantance irin barnar da maharan suka yi.

Kara karanta wannan

Niger: Dubun basarake ta cika, an cafke Sarki kan zargin taimakawa ta'addanci

Yan sanda
An bukaci kafa caji ofis a unguwar da aka kai hari Abuja. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Bukatar ofishin ‘yan sandan Abuja

Ƙaramar hanyar da ke kaiwa zuwa unguwar Grow Homes ta kasance cikin matsanancin hali, wanda ke hana isowar jami’an tsaro da wuri idan wani lamari ya taso.

Mazauna unguwar sun roki gwamnatin tarayya da ta birnin Abuja da su hanzarta gyara hanyar, tare da gina ofishin ‘yan sanda a yankin domin karfafa tsaro.

A cewar wani mazaunin yankin:

“Gwamnati ta taimaka ta gyara hanya domin motocin jami'an tsaro su rika shiga da sauri. Kuma muna rokon a kafa ofishin ‘yan sanda nan kusa domin kawo taimakon gaggawa,”

Wannan harin na zuwa ne a wani lokaci da hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga ke ƙaruwa a sassa daban-daban na Najeriya, duk da ikirarin gwamnati cewa tana kokarin dakile su.

An kona gidaje a harin da aka kai Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa an kai hari kan wasu mutane a jihar Taraba yayin da aka karya yarjejeniyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai sabon hari Kogi, sun sace babban jami'in soja da ya yi ritaya

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Karim Lamido bayan da aka samu sabani tsakanin manoma da makiyaya.

Sojoji sun kama wasu mutane dauke da makamai yayin da aka same su suna kona gidajen wasu mazauna yankin da lamarin ya faru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng