"An Talauta 'Yan Najeriya": Tsohon Ministan Buhari Ya Yi Raga Raga da Gwamnatin Tinubu
- Tsohon ministan wasanni a zamanin Muhammadu Buhari ya taso gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaba
- Solomon Dalung ya caccaki gwamnatin Tinubu saboda wahalar da ƴan Najeriya ke sha a ƙarƙashinta a shekara biyun da ta yi a mulki
- Tsohon ministan tarayyan ya nuna cewa duk da irin dukiyar da ƙasar nan ke samu, ƴan Najeriya na cikin halin talauci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon minista a gwamnatin Muhammadu Buhari, Solomon Dalung, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu.
Solomon Dalung ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya jefa ƙasar nan cikin wani mawuyacin hali a shekara biyun da ya yi a kan mulki.

Source: Facebook
Tsohon ministan wasannin ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Dalung ya ce kan gwamnatin Tinubu?
Ya bayyana cewa a cikin shekara biyu na mulkin Tinubu, ba a ɗauki wasu matakai na kyautata rayuwar al'umma ba.
Tsohon ministan ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaza wajen inganta rayuwar ƴan Najeriya.
“To gaskiya, cikin shekaru biyu da suka gabata, ina ganin ƙasar nan ba ta taɓa shiga wani mawuyacin hali kamar yadda take yanzu ba dangane da mulki nagari, domin mulki nagari yana inganta rayuwar al’umma."
"Alamomin mulki nagari kuwa su ne gaskiya, riƙon amana da adalci."
“Yanzu haka, waɗannan abubuwa uku a cikin shekara biyu da suka gabata ba a ganin su ko kaɗan. Don haka, idan zan ƙimanta gwamnatin nan dangane da mulki nagari, zan ce sun kasa matuƙa. Sun samu ƙasa da kaso 10% cikin 100%."
- Solomon Dalung
Dalung ya ce an talauta ƴan Najeriya
Tsohon ministan ya kuma soki gwamnatin Tinubu kan jefa ƴan Najeriya cikin ƙangin talauci, duk da kuɗin da take samu.
Ya nuna cewa saboda tsabar talauci, ƴan Najeriya har mutuwa suke yi saboda yunwa.

Source: Facebook
“A cikin shekaru biyu da suka gabata, ƙasar nan ta fi samun kuɗi fiye da kowanne lokaci, musamman bayan cire tallafin man fetur."

Kara karanta wannan
"Tinubu ya dage sai an magance matsalar tsaro a 2025," Badaru ya faɗi halin da ake ciki
"Amma a halin yanzu, alamomin talauci sun fi muni fiye da ko yaushe a tarihin ƙasar nan. Tare da hauhawar farashi mai tsanani, magance talauci ya zama abin da ba zai yiwu ba domin ƴan Najeriya na mutuwa saboda yunwa da fatara."
“Ko lokacin yaƙin basasa ƴan Najeriya ba su sha wahala irin wannan ba, sai dai watakila a wuraren da yaƙin ya shafa kai tsaye, wato tasirin yaƙin a kan al’umma da muhallinsu."
"Amma yanzu ba mu cikin yaƙi, amma duk da haka, ƴan kasa ba za su iya ciyar da kansu ba. Ina ganin ƙoƙarin da gwamnati ke cewa tana yi wajen rage talauci ba gaskiya ba ne."
- Solomon Dalung
Ba a fara mulkin Tinubu da kyau ba
Tun da Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a watan Mayu 2023, ‘yan adawa da masu sharhi suka fara nuna damuwa da hanyoyin da gwamnatinsa ke tafiyar da lamurran kasa, musamman bayan cire tallafin man fetur ranar farko da ya kama aiki.
Wannan mataki ne da aka ce ya bude kofa ga hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa, inda mutane da dama suka fara korafi kan karancin abinci, matsin lamba a harkar sufuri da rashin biyan albashi yadda ya kamata.
A shekarar farko, Tinubu ya fara daukar matakai da dama da ya bayyana a matsayin gyare-gyare, kamar sabbin haraji, da kara kudin wutar lantarki.
Sai dai, ‘yan adawa suna cewa wadannan matakai sun fi cutar da talakawa fiye da yadda suke amfana da su. Suna kallon gwamnatin a matsayin wadda ba ta da tausayi, kuma ba ta bai wa mutane damar shan iska.
A cikin shekarar 2024 zuwa 2025, rahotanni sun karu game da take hakkin ma’aikata, cire tallafin noma, da kuma kin sauraron koke-koke daga kungiyoyin fararen hula.
Wasu na kallon wannan a matsayin fara nuna karfin iko da rashin la'akari da muradin jama’a, lamarin da ya kara kara wa ‘yan adawa kwarin gwiwar caccakar gwamnatin Tinubu.
Dalung ya ja kunne kan sanya dokar ta ɓaci
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan wasanni, Solomon Dalung, ya nuna damuwa kan rikicin masarautar Kano.
Solomon Dalung ya yi gargaɗin cewa idan ba a yi taka tsan-tsan ba, ana iya amfani da rikicin don ƙaƙaba dokar ta ɓaci a jihar Kano.
Tsohon ministan ya yi wannan gargaɗin ne bayan Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero sun shirya gudanar da hawan Sallah.
Asali: Legit.ng

