'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Katsina, an Samu Asarar Rayuka
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan jami'an rundunar tsaron jihar Katsina (C-Watch)
- Miyagun ƴan bindigan sun hallaka jami'an tsaron na C-Watch bayan sun yi musu kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Matazu
- Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kai ziyara inda lamarin ya auku don ganewa idonsa irin ɓarnar da ƴan bindigan suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun kashe jami’an tsaro guda biyar na rundunar tsaron jihar Katsina (C-Watch).
Ƴan bindigan sun kashe jami'an tsaron ne a wani mummunan harin kwanton bauna da suka kai a ƙauyen Maharba da ke ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Source: Twitter
Gwamna Radda ya je ziyarar gani da ido
Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Katsina, Ibrahima Kaulaha Mohammed ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na Facebook
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci wata babbar tawagar tsaro zuwa yankin a ranar Juma’a domin tantance ɓarnar da aka yi da kuma duba matakan tsaro da ake dauka a halin yanzu.
Yadda ƴan bindiga suka kashe jami'an tsaro
Jami’an da aka kashe, ciki har da kwamandan C-Watch, Mallam Sanusi, an bayyana cewa suna kan hanyar kai ɗauki ne lokacin da ƴan bindigan da yawansu ya kai 20, ɗauke da bindigogi a kan babura, suka yi musu kwanton ɓauna a bakin wani rafi.
Ƴan bindigan sun ɓuya ne a cikin bishiyoyin mangwaro da ke kusa da wurin kafin su kai harin. Bayan kisan, sun ƙona motar Hilux da jami’an tsaron ke ciki.
Ya ce har lokacin da Gwamna Radda ya isa wurin, ragowar motar da aka ƙona tana ci da wuta.
Gwamna Radda ya samu rakiyar kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Dr. Nasiru Danmusa, kwamishinan ƴan sanda, daraktan hukumar DSS, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir, da sauran manya ƙusoshi.
Shugaban ƙaramar hukumar Matazu, Alhaji Shamsudeen Sayaya ya jagoranci Gwamna Radda zuwa wurin da ƴan bindigan suka kai harin.

Source: Facebook
Gwamna Radda ya yi Allah wadai da harin
Yayin da yake magana da ƴan jarida, Gwamna Radda ya yi Allah wadai da harin wanda a bayyana a matsayin babban rashi ga jihar Katsina.
Gwamna Radda ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ƙara ƙaimi wajen ganin ta kare dukkan ƙauyukan da ke jihar.
“Mun zo nan ba kawai don duba abin da ya faru ba, amma domin tabbatar da cewa irin wannan hari bai sake faruwa ba. Za mu sake nazari tare da karfafa tsarin tsaro. Wannan nauyi ne da ya rataya a wuyar mu ga waɗannan jaruman da iyalansu."
- Gwamna Dikko Radda
Ƴan bindiga sun kashe manoma a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan sun kashe manoma a wani da suka kai a jihar Katsina.
Ƴan bindigan sun hallaka manoman ne guda uku bayan sun farmake su lokacin da suke aiki a gonakinsu a ƙaramar hukumar Kankara.
Dakarun sojoji sun yi yunƙurin kai ɗauki bayan samun rahoton harin amma kafin su isa wurin, ƴan bindigan sun tsere zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng

