Daga Ƙara Aure, Mata 2 Sun Jefa Kansu a Matsala domin Gamsar da Miji da Kayan Mata

Daga Ƙara Aure, Mata 2 Sun Jefa Kansu a Matsala domin Gamsar da Miji da Kayan Mata

  • An kwantar da wasu matan aure biyu a asibiti sakamakon shan maganin mai kayan mata bayan mijinsu ya ƙara aure a Abuja
  • Mijin matan, Musa Muhammad ya ce matansa sun sha maganin ne domin ƙara ƙarfin sha'awa amma kuma suka kare a wahala
  • Ya bayyana cewa matan sun rasa wasu abubuwa a jikinsu sakamakon shan kayan matan wanda ta kai ga yi masu tiyata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Matan aure biyu da ke zaune a unguwar Dakwa, karamar hukumar Bwari ta Abuja, sun gamu da mummunan ƙaddara bayan mijinsu ya ƙara aure.

Matan sun sha wani ruwan magani mai ƙarfi da aka sani da kayan mata domin ƙara ƙarfin sha’awa da nufin jan ra'ayin mijinsu a harkar kwanciyar aure.

Taswirar Abuja.
Matan aure 2 su jefa kansu a matsala bayan mijinsu ya yi amarya a Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an garzaya da matan biyu, kishiyoyin juna zuwa asibitin bayan shan maganin mai kayan mata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hare haren ramuwar gayya a Zamfara, an hallaka bayin Allah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matan aure 2 sun gamu da illar kayan mata

An ruwaito cewa tun farko matan sun yi haka ne bayan an ɗaura auren mijinsu da wata budurwa a matsayin matarsa ta uku daga garin Gusau, Jihar Zamfara.

Rahoton ya bayyana cewa kayan matan da suka sha, wanda aka fi sani da kayan ƙarfafa sha’awa ana danganta su da haɗurra ga lafiya, har ma da janyo illa ga haihuwa.

Mijin matan, Musa Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, inda ya ce matansa biyu sun sha maganin ne kwana uku bayan ya yi amarya.

Yadda matan suka jefa kansu a matsala a Abuja

Ya ce bayan sun kwankwaɗi maganin, sai suka shiga cikin wani hali na ciwon ciki mai tsanani, har aka kai su wani asibiti a Madalla, jihar Neja.

Musa ya ce:

“An kira ni daga gida, aka faɗa kani cewa matana biyu ba su da lafiya, domin na kwana ne a gidan amarya. Na isa na same su suna birgima a ƙasa suna kuka da ciwon ciki.

Kara karanta wannan

Kwamacala: Abin kunya ya faru da aka kai mata kotu kan zargin auren maza 2 a Kano

"Na kira wata ma'aikaciyar jinya ƴar unguwarmu, amma duk da ta sa masu ruwa, babu alamun sauƙi, nan take na yi hanzarin ɗaukarsu zuwa asibiti."
"Bayan an kai su asibiti aka gano cewa maganin da suka sha ya lalata wasu gabobin jikinsu, har sai da aka yi musu tiyata. An sallame su daga asibitin bayan mako guda.

Musa ya bayyana cewa mai maganin da ke basu kayan mata ta saba ba su ruwan hadi, amma wannan karon ta basu garin hadin wanda suka gauraya da madara.

Shin amfani da kayan mata yana illa?

A cewarsa, hakan ne ya haifar masu da ciwon ciki wanda ya jawo masu matsala mai girma ga lafiyarsu.

A halin yanzu ana neman wadda ta ba su maganin domin gudanar da bincike da kuma hana ta cutar da wasu mata.

A nata ɓangaren, wata likita, Dr. Taiye Anifowose, ta yi gargaɗi kan shan irin waɗannan magunguna da ake kira kayan mata.

Dr. Taiye Anifowose ta ce magungunan suna da haɗari ga gabobin jiki, musamman ma na haihuwa don haka ya kamata a guje masu.

Kara karanta wannan

Wani ɗan sanda ya durƙusa ya ɗaurewa Ganduje takalmi, bidiyo ya ja hankalin jama'a

Matar aure ta kashe mijinta a Yobe

A wani labarin, kun ji cewa wata matar aure, Zainab Isah, ƴar kimanin shekara 22 a duniya ta hallaka mijinta a jihar Yobe.

Matar dai da daɓawa mijinta, Ibrahim Yahaya wuƙa, wanda ya yi sanadin mutuwarsa bayan wata sa'insa ta haɗa su.

Tuni dakarun ƴan sanda suka kama matar da ake zargin kuma sun yi alƙawarin gudanar da bincike kafin gurfanar da ita a gaban kotu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262