Miyagu Sun Tare Jirgi a Najeriya, Sun Yi Awon Gaba da Fasinjoji Sama da 10
- Ƴan fashin teku sun tare jirgin ruwa, sun yi awon gaba da fasinjoji 13 a kogin Idaka da ke ƙaramar hukumar Okrika a jihar Ribas
- Maharan sun kuma kwace wasu jiragen ruwa biyu da suka ɗauko kayayyaki amma daga bisani an ji cewa an yi nasarar ƙwato su
- Shugaban kungiyar ma'aikatan sufurin ruwa (NWU) ya nemi Kantoma ya gaggauta ɗaukar mataki domin abin na neman wuce gona da iri
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Wasu mahara da ake kyautata zaton ƴan fashin teku ne sun tare jirgin ruwa a yankin karamar hukumar Okrika da ke jihar Ribas.
'Yan fashin tekun sun sace fasinjoji 12 da direbansu a cikin wani kwale-kwale a kan Kogin Isaka da ke karamar hukumar Okrika a jihar da ke Kudancin ƙasar nan.

Kara karanta wannan
Bincike: Abubuwa 2 da suka jawo jirgi ya yi hatsari ɗauke da shugaban bankin Access

Source: Original
Rahotan jaridar Leadership ya nuna cewa wadanda aka sace suna kan hanyarsu ta zuwa garin Bille da ke cikin karamar hukumar Degema a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mahara sun sace fasinjojin jirgi a Ribas
Bayanai sun tabbatar da cewa matafiyan na cikin tafiya a cikin ruwa ne kwatsam maharan suka tare jirginsu da yammacin ranar Talata da ta shuɗe.
Bayan haka, an kuma bayyana cewa 'yan fashin sun kwace wasu jiragen ruwa guda biyu da ke cike da kayayyaki a jihar Ribas.
Channels TV ta ruwaito cewa jiragen da suka ɗauko kayayyakin na kan hanyarsu ta zuwa Cawthorne Channel da kuma Bonny Island duk a jihar Ribas lokacin da suka faɗa hannun maharan.
Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Sufurin Ruwa (MWU) a jihar Ribas, Mista Israel Pepple, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a birnin Fatakwal.
Yadda ƴan fashin suka farmaki jirage 3
“Fasinjoji 12 da direbansu na can a hannun ƴan fashin da suka yi garkuwa da su yanzu haka, amma an samu nasarar kwato jirage biyu da aka sace.
"Kwale-kwale guda uku ne maharan suka farmaka, ɗaya na hanyar zuwa Cawthorne Channel, ɗaya ya nufi Bille, yayin da ɗayan kuma na hanyar zuwa Bonny.
“Wanda ya nufi Bille shi ne ƴan fashin tekun suka tare kuma suka tafi da fasinjoji da direba, sauran biyun kuma suka ƙwace su saboda suna ɗauke da kayayyaki."
- In ji Mista Israel Pepple.

Source: Getty Images
An buƙaci shugaban riko ya ɗauki mataki
Pepple ya roki shugaban riko na Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), da ya ƙara tsaurara matakan tsaro a hanyoyin ruwa, musamman a yankunan Bille da Isaka.
“Muna kira ga shugaban riko da ya ɗauki mataki domin wannan lamari yana neman wuce gona da iri,” in ji Pepple.
Ibok-Ete Ibas ya sha alwashin magance matsalolin rashin tsaro a Ribas da ya shiga ofis.
Jiragen ruwa sun yi hatsari a Bayelsa
A wani rahoton, kun ji cewa wasu jiragen ruwa biyu sun yi taho mu gama a gabar ruwan da ke yankin Ijaw ta Kudu a jihar Bayelsa.
Mutum biyu sun mutu yayin da wasu fasinjoji 13 da ke cikin jiragen suka nutse a ruwa har yanzu ba su samu nasarar ciro su ba.
Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da wani jirgin ruwa mai gudu dauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
