Tirkashi: An Kafa Wata Gwamnati a Najeriya, Za a Bi Diddigin Ayyukan Tinubu
- Farfesa Pat Utomi ya ƙaddamar da gwamnatin sa ido mai mambobi daga jam'iyyun adawa, domin sa ido kan ayyukan gwamnatin tarayya
- Utomi ya ce manufofin gwamnati sun ƙara jefa mutane a talauci, sun ƙarfafa ta'addanci, abin da ya ce ya zama dalilin kafa gwamnatin sa ido
- Sai dai gwamnati, ta bakin ministan labarai, Mohammed Idris, ta nuna adawa da matakin Utomi, inda ta ce ba mulkin Firaminista ake yi ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Masanin tattalin arziki kuma ɗan gwagwarmaya, Farfesa Pat Utomi, ya ƙaddamar da gwamnatin sa ido, wacce ta ƙunshi mambobi daga jam’iyyun adawa daban-daban.
Farfesa Pat Utomi ya kaddamar da wannan gwamnatin sa idon a yanar gizo a daren ranar Litinin, inda ya ce za ta rika sa ido kan ayyukan gwamnati tare da ba da shawarwari.

Source: Twitter
Gwamnati ta yi martani kan kafa gwamnatin sa ido
Amma cikin gaggawa, ministan yada labarai, Mohammed Idris, a zantawarsa da The Punch, ya nuna rashin amincewar gwamnati kan wannan matakin.
Mohammed Idris, ya ce:
“Rashin sanin ya kamata ne a ce lokacin da ƙasarmu ke shirin yin bikin cika shekaru 26 na shugabancin dimokuraɗiyya, wani ya yi tunanin kafa wata 'gwamnatin sa ido'.
“Najeriya ba ta na kan tsarin firaminista ba ne inda ake gudanar da irin wannan gwamnatin, kuma babu tanadin hakan a cikin dokokinmu.
“Duk da yake siyasar adawa muhimmiyar sifa ce ta dimokuraɗiyya, amma dole ne a kowane lokaci a gudanar da ita bisa dokokin da suka dace.
"Majalisar tarayya tana da 'yan majlisun adawa sosai, inda nan ne ya kamata ya zama wuri mafi dacewa don yin sa-in-sa da sanya ido kan ayyukan gwamnati."
Farfesa ya kalubalanci manufofin Tinubu
Sai dai, Utomi ya kare matakinsa na kafa gwamnatin sa ido a Najeriya, yana mai cewa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu sun ƙara ta'azzara talauci a kasar.
Ya ce manufofin sun tilasta kamfanoni masu yawa tattara kayansu tare da barin ƙasar, kuma sun ƙarfafa ta'addanci a jihohin Benue da Filato, tare da ƙaruwar rashin tsaro da cin hanci da rashawa a faɗin ƙasar.
Masanin tattalin arzikin ya nuna damuwarsa game da abin da ya kira komawar gwamnati ga yaɗa farfaganda da kuma murƙushe ra'ayoyin adawa.

Source: Twitter
Dalilin kafa gwamnatin sa ido - Utomi
A cewar Utomi:
"Yawan sauya shekar da aka yi kwanan nan zuwa jam'iyyar APC ya ƙara tabbatar da cewa ba a yi komai yadda ya kamata ba a dimokuraɗiyyar Najeriya."
Ya ce an ƙirƙiri gwamnatin sa ido, wacce ta ƙunshi fitattun mutane daga jam’iyyun adawa da dama don mayar da martani ga abin da ya kira 'matsalolin ƙasa'.
“A yau, ina gabatar da wannan gwamnatin sa idon bayan ganin koke-koken jama'a game da halin da suke ciki. Ina ƙalubalantar ku da ku, da ku zo mu farkar da waɗannan mutanen da ke azurta kansu daga man kasarmu."
- Farfesa Pat Utomi.
APC za ta kafa gwamnatin sa ido a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar APC a Kano ta bayyana shirinta na kafa gwamnatin basaja domin bin diddigin ayyukan gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Ƙungiyar za ta tura wakilanta zuwa dukkan ma’aikatun gwamnati da ke jihar domin bibiyar yadda ake aiwatar da ayyuka, sannan su fitar da rahotannin adawa akai-akai.
Shugaban ƙungiyar na APC, Alhaji Usman, ya bayyana cewa za su sanar da jama’a cikakken tsarin yadda za su gudanar da wannan aikin nan gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


