Peter Obi Ya Gano Yadda Gwamnatocin Najeriya ke Jawo Talauci
- Tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya zargi gwamnati da rashin gudanar da mulki yadda ya kamata, wanda ya haifar da tsananta talauci
- Ya ce tilas ne 'yan Najeriya musamman masu arziki su sadaukar da wani abu domin ceto al’umma daga fatara da rikice-rikice da ya addabi kowa
- Mista Obi ya zargi gwamnatocin Najeriya da barin aikin da ya rataya a wuyansu ga kungiyoyi da coci, yayin da jama'a ke cikin mawuyacin hali
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Enugu – Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya ce talauci na kara kamari a Najeriya ne saboda gwamnatoci sun yi watsi ingantaccen shugabanci.
Obi ya bayyana cewa dole yan kasar nan masu abin hannu su sadaukar da wani bangare na jin dadinsu domin su fitar da al'umma daga kangin talauci da kawo karshen rikice-rikice.

Source: Facebook
The Guardian ta ruwaito cewa tsohon gwamnan Anambra ya bayyana hakan ne a jiya bayan ya bayar da gudummawar Naira miliyan 40 ga cocin Anglican na Diocese da jami'ar Godfrey Okoye University aEnugu.
Kowanne daga cikinsu ya samu Naira miliyan 20 domin taimakawa da ayyukan kiwon lafiya da suke aiwatarwa.
Peter Obi ya caccaki gwamnati a Najeriya
Peoples Gazette ta wallafa cewa yayin bayar da gudummawar, Obi ya nuna bakin ciki cewa coci-coci da kungiyoyi masu zaman kansu suna gudanar da ayyukan da ya kamata gwamnati ta rika yi.
Ya ce:
“An ce al’umma mai ingantaccen lafiya, al’umma ce mai arziki. Don haka dole mu zuba jari a fannin. Kamar yadda kuke gani, na shiga kawane coci, na ga yadda suke aiki a wannan bangaren."
Peter Obi na son a karfafa ilimi
Peter Obi ya kara da cewa al'umma tana samun ci gaba ne matukar ilimi ya samu tagomashi, wanda haka ne ya dace da Najeriya.

Source: Facebook
Ya ce:
“Haka kuma, coci na yin aiki babba a fannin ilimi wanda ba za a misaltawa ba. Don haka dole mu hada kai da coci da kungiyoyin sa-kai domin shawo kan wannan matsala. Wannan aikin ya shafi kowa.”
A makarantar koyar da aikin jinya ta Godfrey Okoye, Obi ya karfafa gwiwar daliban da su kasance masu himma da jajircewa.
Hakeem Baba ya shawarci Obi, Kwankwaso
A baya, mun wallafa cewa Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP da Peter Obi na LP da su hakura da neman takarar shugabancin kasa a zaben 2027.
Dr. Baba-Ahmed ya jaddada cewa lokaci ya yi da tsofaffin ‘yan takara za su ja daga gefe su bai wa matasa dama su fito takara domin ceto Najeriya daga halin da take ciki na kunci a yanzu.
Ya kara da cewa wadanda suka taba takarar shugaban kasa a baya sun yi iya bakin kokarinsu amma ba su kawo wani gagarumin sauyi ba, don haka lokaci ya yi da za su ba wasu dama.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

