Sanusi II Ya Naɗa Sabon Turakin Kano yayin da Ɗansa Ya Ziyarci Shugaban APC
- Ko da yake rikicin masarautu bai kare ba a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ci gaba da nade-naden sarauta a fadar jihar
- Sanusi II ya nada sabon Galadiman Kano domin maye gurbin marigayi Abbas Sanusi, kuma ya nada Mahmud Ado Bayero a matsayin Turakin Kano
- Tafidan Kano, Malam Adam Lamido Sanusi, ya kai ziyara ga Hon. Abdullahi Abbas a ranar Litinin 5 ga watan Mayu, 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Duk da cewa ba a gama da rigimar masarautu ba a Kano, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi nade-nade kamar yadda aka saba.
Nadin baya-bayan nan shi ne na Galadiman Kano domin maye gurbin marigayi, Alhaji Abbas Sanusi da ya riga mu gidan gaskiya.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shafin Dala FM Kano ta wallafa a manhajar Facebook a yau Talata 6 ga watabn Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarki Muhammadu Sanusi II ya isa Tunisia
Wannan na zuwa ne bayan Sarki Muhammadu Sanusi II, ya isa kasar Tunisia domin halartar babban taron zuba jari da ciniki na Afrika (FITA2025).
An ce taron zai gudana ne a ranakun 6 zuwa 7 ga watan Mayun shekarar 2025, a babban otal din Radisson Blu da ke birnin Tunis.
Basaraken ya samu rakiyar manyan masu mukamin gargajiya daga Kano, ciki har da Sarkin Shanun Kano, Nazir Halliru, da Jarman Kano.
Adam Sanusi Lamido ya ziyarci shugaban APC
Hakan ya biyo bayan ziyarar da 'dan Sarki Muhammadu Sanusi II ya kai ga shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas.
Shafin Sanusi II Dynasty ya wallafa a manhajar Facebook cewa Mai girma, Tafidan Kano, Adam Lamido Sanusi ya kai ziyara ta musamman ga shugaban APC a jihar, Hon. Abdullahi Abbas.
Sanarwar ta ce:
"Mai Girma Tafidan Kano, Adam Lamido Sanusi ya ziyarci Hon. Abdullahi Abbas Sanusi a ranar Litinin 5 ga watan Mayun 2025."

Source: Twitter
Sarki Sanusi II ya nada Turakin Kano
Sarki Sanusi II ya yi nade-naden ne yayin da shi ma Aminu Ado Bayero ya nada na shi Galadiman Kano a ranar Juma'a 2 ga watan Mayun 2025 da ta gabata.
Daga cikin nade-naden akwai sabon Turakin Kano, Alhaji Mahmud Ado Bayero domin ci gaba da gudanar da sarauta.
A cikin sanarwar, shafin ya ce:
"Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II Phd, CON ya nada Alh Mahmud Ado Bayero a matsayin sabon Turakin Kano."
Yan sanda sun kulle gidan Galadiman Kano
A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sanda ta mamaye gidan Galadiman Kano da ke Galadanci, a Gwale, bayan naɗa Galadima biyu da aka yi a ranar Juma'a 2 ga watan Mayun 2025.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya nada Munir Sanusi Bayero a Gidan Rumfa, yayin da Aminu Ado Bayero ya nada Sanusi Ado Bayero a Nasarawa.
Iyalan gidan Galadima sun ce ba su da hannu a rikicin, amma suna cikin damuwa kan yadda siyasa ke rushe musu zumunci da al’ada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

