Lauyoyi Sun Mamaye Majalisar Tarayya, Suna So a Kwace Ikon Majalisun Jihohin Arewa 2
- Lauyoyi sama da 1000 sun yi dandazo a harabar majalisar tarayya, suna neman a kwace ikon majalisun dokokin Benue da Zamfara
- Sun nuna damuwarsu kan yadda aka dakatar da 'yan majalisa 23 a jihohin Zamfara da Benue saboda sun samu sabani da gwamnoni
- Lauyoyin sun yi gargadin cewa rashin magance matsalar na iya haifar da dokar ta-baci a jihohin biyu, kuma ya shafi majalisar tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Talata, lauyoyi sama da 1000 daga sassan Najeriya sun mamaye majalisar tarayya, suna neman majalisar ta kwace ikon majalisun dokokin Benue da Zamfara.
Yayin zanga-zagar luma, lauyoyin sun ce majalisun Benue, Zamfara yanzu ba sa iya gudanar da ayyukansu saboda rikicin cikin gida da kuma zargin tsoma bakin gwamnoni.

Source: UGC
Abin da ya sa lauyoyin zanga-zanga a majalisa
A cikin wata takardar korafi, lauyoyin sun nuna damuwarsu kan yadda aka dakatar da wasu 'yan majalisa 10 a Zamfara tun Fabrairu 2024, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun yi ikirarin cewa an dakatar da 'yan majalisar ne bisa zargin umarnin gwamnan jihar, Dauda Lawal saboda suna magana kan karuwar rashin tsaro a jihar.
A Benue kuma, lauyoyin sun bayyana cewa an dakatar da 'yan majalisa 13 saboda zargin kin bin umarnin Gwamna Hyacinth Alia na dakatar da babban alkalin jihar.
An nemi a kwace ikon majalisun Benue, Zamfara
Lauyoyin, karkashin jagorancin Barista Sambari Benjamin, sun bukaci majalisar tarayya da ta yi amfani da sashe na 11(4) na kundin tsarin mulkin don kwace ikon majalisun jihohin biyu.
Lauyoyin sun yi gargadin cewa idan ba a magance wannan matsalar ba, hakan na iya haifar da ayyana dokar ta-baci a jihohin biyu.
Sun kuma nuna damuwarsu cewa rikicin na iya yaduwa har zuwa majalisar tarayya, wanda hakan zai iya zama babbar barazana ga dimokuradiyyar kasar baki daya.
Lauyoyin sun roki Godswill Akpabio, da ya shiga tsakani cikin gaggawa tare da kwace ikon majalisun Benue da Zamfara domin dawo da zaman lafiya a jihohin biyu.

Source: Twitter
Lauyoyi sun kawo dokar kwace ikon majalisa
Wani sashe na takardar korafin na cewa:
"Bayan da majalisar tarayya ta amince da dokar ta-bacin da aka ayyana a Rivers, muna matuƙar fargabar cewa jihohin Benue da Zamfara ma na iya shiga irin wannan yanayin ba da jimawa ba.
"Amma za a magance haka idan an dauki matakin cikin gaggawa ta hanyar kwace ikon majalisun dokokin jihohin biyu domin gyara matsalolin da ke faruwa.
"Da wannan, mu ke neman majalisar ta yi amfani da sashe na 11 (4) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya domin ta karbe ragamar ayyukan majalisun jihohin biyu."
Ana so Tinubu ya ayyana dokar-ta-baci a Zamfara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata ƙungiyar Arewa mai suna CAJ ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a Zamfara.
CAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da mulkin kama-karya, tana mai cewa jihar ta daina ci gaba a halin yanzu, musamman saboda rashin tsaro.
Ƙungiyar ta CAJ ta kuma bayyana cewa 'yan bindiga sun karɓi ikon garuruwa suna karɓar haraji, yayin da jami'an gwamnatin jihar ke amfana daga haramtacciyar hakar ma'adinai.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

