Tinubu Ya Lalata Shirin Atiku, Ƴan Majalisar Wakilai 6 Sun Fice daga PDP zuwa APC

Tinubu Ya Lalata Shirin Atiku, Ƴan Majalisar Wakilai 6 Sun Fice daga PDP zuwa APC

  • 'Yan majalisar wakilai shida daga Delta karkashin PDP sun koma APC, sakamakon rikicin shugabanci da suka ce ya mamaye jam'iyyar
  • Wannan na zuwa ne bayan gwamnan Delta da tsohon gwamna sun koma APC, yayin da 'yan majalisar LP biyu daga Enugu suka koma PDP
  • Duk da sauya shekar da ake yi, Bukola Saraki ya nuna kyakkyawan fata game da makomar PDP, yana mai cewa za su sake tsara jam'iyyar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Talata, wasu 'yan majalisar wakilai shida daga jihar Delta karkashin jam'iyyar PDP sun sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Haka kuma, jam'iyyar LP ta Peter Obi ta rasa 'yan majalisarta biyu daga jihar Enugu zuwa PDP.

'Yan majalisar wakilai 8 sun sauya sheka zuwa APC, PDP a Abuja
Zauren majalisar wakilan tarayya, Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

'Yan majalisar wakilan Delta 6 sun koma APC

Shugaban majalisar, Tajudeen Abbas, ya sanar da sauya shekar tasu a zaman majalisar na ranar Talata, kamar yadda Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Siyasa ta dauki zafi: Kakakin majalisa da ciyamomi 17 sun fice daga PDP zuwa APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nicholas Mutu (Bomadi), wanda ya fi kowa dadewa a majalisar kuma shugaban kungiyar 'yan majalisar Kudu, ya jagoranci wadanda suka sauya shekar daga Delta.

An rahoto cewa Hon. Mutu ya kasance yana wakiltar mazabarsa karkashin PDP tun daga shekarar 1999 har zuwa yau Talata da ya koma APC.

Sauran 'yan majalisar da suka sauya shekar sun hada da Nnamdi Ezechi (Ndokwa/Nkwuani) sai Jonathan Okodiko (Isoko).

Har ila yau akwai Thomas Eriyetomi (Warri), Julius Pondi (Burutu), da Victor Nwokolo (Ika Arewa da Kudu).

Dalilin 'yan majalisar na barin PDP zuwa APC

A cikin wasikun murabus dinsu da shugaban majalisar ya karanta, 'yan majalisar sun bayyana rikicin jam'iyyar da ya ki ci ya ki cinye ne dalilin sauya shekararsu.

Hakazalika, sun shaida cewa PDP ta dare gida biyu a jihar Delta, kuma an gaza shawo kan matsalar, wanda hakan ya tilastasu komawa APC.

Wannan dai na zuwa ne 'yan kwanaki da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon gwamna, Ifeanyi Okowa, suka sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

"Guguwar Tinubu": Kakakin majalisar dokoki da ƴan majalisa 21 sun fice daga PDP zuwa APC

'Yan majalisar LP 2 sun koma PDP

Sai dai kuma a hannu daya, mun ruwaito cewa, an samu 'yan majalisa biyu daga jihar Enugu karkashin jam'iyyar LP da suka sauya sheka zuwa PDP.

'Yan majalisar LP da suka koma PDP sun hada da Mark Obetta (Nsukka/Igboeze Kudu ta Enugu) da Dennis Agbo (Igbo Eze Arewa/Udenu).

Wadanda suka sauya shekar sun danganta matakinsu da rikicin da ke addabar LP, da kuma bukatar samun jam'iyya da ta dace da wakilcin mazabunsu.

'Yan majalisun wakilai 8 daga jam'iyyu daban daban sun sauya sheka zuwa APC da PDP
Zauren majalisar wakilan tarayya, Abuja. Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Wani dan majalisa daga jihar Imo, Ikenga Ugochinyere, ya ce gwamnoni biyu da 'yan majalisa 40 za su fice daga PDP zuwa APC nan ba da jimawa ba, yana mai nuni ga wani rikici mai zurfi a cikin jam'iyyar.

Bukola Saraki ya doge kan farfadowar PDP

Duk da sauya shekar da ake yi, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya nuna kyakkyawan fata game da makomar PDP.

Bukola Saraki ya jaddada cewa za su sake tsara PDP, kuma duk wadanda suke son ficewa daga jam'iyyar to su hanzarta yin hakan tun wuri.

Kara karanta wannan

An dakatar da manyan alkalan Najeriya 3, za su rasa albashin wata 12

"Za mu gyara Najeriya" - Saraki ya fadi shirin PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya jaddada bukatar sake gina PDP kan kyakkyawan tunani, falsafa da manufofi.

A cewar Saraki, akwai bukatar PDP ta daina batun wanda zai tsaya takarar kansila, ko gwamna, ko shugaban kasa a 2027, ta canja salon da zai ba ta nasara gaba daya.

Yayin da ya ce jam'iyyar ce kawai za ta iya gyara Najeriya, Saraki ya ce za su sake gina PDP, su daidaita alkiblarta domin ganin cewa ta sake kabar mulki daga APC a 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com