NiMet Ta Lissafa Jihohin Najeriya da Za a Sheka Ruwa Hade da Tsawa a Kwanaki 3

NiMet Ta Lissafa Jihohin Najeriya da Za a Sheka Ruwa Hade da Tsawa a Kwanaki 3

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen haduwar hadari mai hade da tsawa a sassa daban-daban na Najeriya daga ranar Talata zuwa Alhamis
  • A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran saukar ruwa mai hade da tsawa, yayin da wasu jihohin Kudu za su fuskanci hadari tare da walkiya
  • Hukumar ta shawarci jama'a musamman masu fama da matsalar numfashi da su yi taka-tsan-tsan saboda yiwuwar samun iska mai karfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama hade da tsawa a sassa daban-daban na kasar nan daga ranar Talata zuwa Alhamis.

Hasashen yanayin da NiMet ta fitar a ranar Litinin a Abuja ya nuna cewa hadari hade da walkiya da tsawa na iya mamaye Katsina da Kano a ranar Talata.

Kara karanta wannan

An gano illar rikicin filaye a Najeriya bayan an salwantar da rayuka kusan 2000

Hukumar NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama hade da tsawa a wasu jihohin Najeriya
Ruwan sama mai karfi yana sauka hade da tsawa da walkiya. Hoto: Analogu via Getty Images
Source: Getty Images

Hasashen ruwa da tsawa a ranar Talata

Ana kuma tsammanin haduwar hadari da tsawa mai karfi a jihar Taraba da Adamawa da rana da kuma yamma, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran sararin samaniya zai kasance da ɗan hadari, tare da yiwuwar walkiya da tsawa a Nasarawa Kogi, Kwara, Benue, da Abuja.

A Kudancin Najeriya kuwa, ana tsammanin saukar ruwa, sannan tsawa ta biyo baya a Akwa Ibom, Cross River, Rivers da Bayelsa da safe.

Da yammacin ranar kuwa, ana sa ran saukar ruwa da tsawa a Osun, Ekiti, Ondo, Oyo, Edo, Abia, Imo, Bayelsa, Lagos, Delta, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Hasashen yanayin NiMet na ranar Laraba

Ranar Laraba, NiMet ta yi hasashen ruwa hade da tsawa a Arewa. Ana kuma tsammanin hadari da tsawa a Taraba da Adamawa da rana ko yamma.

Kara karanta wannan

Rivers: Komai na iya faruwa da rigima ta kunno kai a kokarin dawo da Fubara

A Arewa ta Tsakiya, ana hasashen hadari hade da tsawa a Abuja, Plateau, Benue, Kogi, Niger da Nasarawa da rana/yamma, inji rahoton PM News.

A Kudu kuwa, ana sa ran hadari a Bayelsa, Cross River, Akwa Ibom da Rivers da safe, daga baya kuma a Ogun, Osun, Ekiti, Ondo, Oyo, Imo, Enugu, Ebonyi, Anambra, Abia, Lagos, Bayelsa, Akwa Ibom, Cross River, Rivers da Delta.`

NiMet ta shawarci mutane su yi taka tsantsan a lokacin wura da tsawa
Shugaban NiMet, Prof. Charles Anosike yayin rangadi a ofishin hukumar na Arewa. Hoto: @nimetnigeria
Source: Twitter

NiMet ta gargadi mutane kan iska mai karfi

Ranar Alhamis, NiMet ta yi hasashen hadari zai hadu a Arewa. A Arewa ta Tsakiya, ana sa ran haduwar hadari da safe, daga baya kuma a samu hadari da tsawa a Abuja, Plateau, Kogi, Kwara, Niger da Nasarawa.

A Kudancin Najeriya, ana sa ran hadari da yiwuwar tsawa da safe a Delta da Bayelsa, daga baya kuma a Osun, Ekiti, Ogun, Oyo, Ondo, Anambra, Abia, Ebonyi, Enugu, Imo, Cross River, Akwa Ibom, Rivers, Edo, Delta, Lagos da Bayelsa.

Hukumar ta shawarci jama'a da su yi taka-tsan-tsan saboda yiwuwar samun guguwa kafin saukar ruwa, musamman ma masu fama da matsalolin numfashi.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da neman hatsabibin ɗan bindiga Bello Turji, yaransa sun yi ta'asa a Sokoto

Sauyin yanayi a Najeriya

Sauyin yanayi na daya daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar Najeriya da sauran kasashen duniya.

Wannan sauyi yana faruwa ne sakamakon karuwar dumamar doron kasa da ke haifar da sauye-sauyen yanayi fiye da yadda aka saba.

A Najeriya, sakamakon sauyin yanayi ya bayyana ta hanyoyi daban-daban kamar: karancin ruwan sama a Arewa, yawaitar ambaliya a Kudu, dumamar iska, da kuma karancin abinci sakamakon tasirinsa ga aikin noma.

Wannan sauyi yana da illa mai yawa a rayuwar yau da kullum: yana haifar da rushewar ababen more rayuwa, cututtuka da ke yaduwa sakamakon ambaliya ko fari, da kuma tasiri ga lafiya musamman ga masu fama da matsalolin numfashi.

Hukumar NiMet tana taka muhimmiyar rawa wajen hasashen yanayi domin ankarar da jama’a kan yiwuwar ruwan sama mai karfi, guguwa, ko tsawa.

Hasashe irin na wannan makon yana da nasaba da sauyin yanayi wanda ke sa ruwan sama ya sauka fiye da kima ko a lokacin da ba a saba ba.

Kara karanta wannan

Al'umma sun samu sauƙi bayan kisan fitinannen ɗan bindiga da ya addabi Arewa

Yin taka-tsantsan da bin shawarar hukumomi kamar NiMet yana taimakawa rage hadurra da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Jihohin Arewa da za a fuskanci zafi mai tsanani

A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta yi gargadi game da tsananin zafin rana da ake sa ran afkuwa a Gombe da wasu jihohi 17 na Arewa.

Hukumar ta bayyana cewa zafin rana zai iya kaiwa digiri 40 a ma'aunin Celsius, wanda zai haifar da rashin jin daɗi da kuma canjin yanayin jikin mutane.

Don haka, NiMet ta shawarci jama'a da su yawaita shan ruwa, su guji fita rana kai tsaye, sannan su kula da yara da tsofaffi a wannan lokacin zafi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com