Za’a sha ruwa da tsawa a Najeriya a gobe Lahadi – Hukumar kula da hasashen yanayi
Hukumar da ke kula da yanayin sararin samaniya na Najeriya (NiMET), tayi hasashen cewa za ayi tsawa da ruwan sama a yankin arewa maso gabas da yankuna da ke kewaye da teku, sannan kuma za a wayi gari da girgije a yawancin yankunan kasar a ranar Lahadi.
A hasashen hukumar NiMET na ranar Asabar a Abuja ta bayyana cewa girgije zai lullube jihohin da ke yankin tsakiya da kuma yiwuwar tsawa da safe.
Hukumar tayi hasashen tsawa a Abuja, Plateau, Kaduna, Benue, Yola, Jalingo da yankin Mambilla da yamma, inda ma’aunin ta ya bayyana cewa za a samu rana daga bisani a yakin Plateau.
A cewar NiMET, za a samu girgije a jihohin Arewa tare da alamun tsawa a Nguru, Damaturu, Bauchi, Kano da Katsina a sa’o’in safe.
Har ila yau NiMET tayi hasashen tsawa a Bauchi, Kano, Katsina da Nguru yayin da sauran yankuna zasu kasance cikin yanayin girgiji da yamma.
KU KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kare mutanenmu – Buhari ga shugabannin ECOWAS
Daga karshe sanarwar hukumar ta bayyana cewa za’a samu matsakaicin ruwan sama a jahohin kudu masu yammacin kasarnan, tare da samun digiri 27 zuwa 32 na yanayi da rana, yayin da yanayin dare zai sauka tsakanin digiri 20 zuwa 23 a ma’aunin Celcius.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng