Shugaba Tinubu Ya Fadi halin da Matsalolin Najeriya Suka Jefa Shi a farkon Mulkinsa

Shugaba Tinubu Ya Fadi halin da Matsalolin Najeriya Suka Jefa Shi a farkon Mulkinsa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce matsalolin da kasar ke fama da su a fannin tattalin arziki sun yi masa yawa a farkon zamansa a ofis
  • Ya bayyana cewa bai ji dadin irin abubuwan da ya rika karanta wa a jaridu a kan matakan da ya dauka wajen gyara tattalin arzikin Najeriya ba
  • Duk da wahalhalun da suka biyo bayan matakan da aka dauka, Tinubu ya ce ya tsaya tsayin daka don ganin Najeriya ta fita daga matsin lamba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kalubalen tattalin arzikin Najeriya a farkon zamanin mulkinsa sun yi masa yawa.

Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai jihar Katsina a karshen mako, inda ya ce sukar shi da ake yi da tsananin kalubalen shugabanci sun jefa shi a cikin damuwa matuka.

Kara karanta wannan

Turji ya zafafa hare-hare a Sakkwato, mazauna kauyuka 20 sun fara kaura

Tinubu
Shugaban kasa ya ce matsalolin Najeriya sun tsorata shi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa Tinubu ya ce tsananin matsalolin da kasar ke ciki sun sanya ya yi tunanin daina karanta jaridu da sauraron labarai gaba ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda matsalar Najeriya ta tsorata Tinubu

Daily Post ta wallafa cewa Shugaban kasa Tinubu ya ce bayanan da yake karantawa a jaridu dangane da matakan da yake dauka a kan tattalin arziki sun firgita shi.

A cewarsa:

“Da muka fara, abubuwa sun yi matukar wahala, har na kusa daina kallon talabijin ko karanta jaridu. Na ji kamar in fitar da rai, amma na tsaya tsayin daka kan matakan da muka dauka, domin na san kwarewar shugaba tana fitowa ne daga iya yanke shawara a daidai lokacin da ya dace.”
“Mun rungumi matsin lambar kuma muka jajirce, yanzu mun fara ganin amfanin hakan.”

Bola Tinubu ya yabi manufofinsa

Sai dai Tinubu ya jaddada cewa tsauraran matakan tattalin arziki da gwamnatinsa ta dauka sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Kara karanta wannan

Rivers: Komai na iya faruwa da rigima ta kunno kai a kokarin dawo da Fubara

Tinubu
Shugaba Tinubu ya ce manufofinsa suna kara karfafa tattalin arziki Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Ya kara da cewa:

“Najeriya tana kan turbar nasara, tattalin arziki yana shiga hayyacinsa, mun riga mun kauce daga hanyar da ta kai ga tabarbarewar tattalin arziki, kuma abubuwa za su ci gaba da kyautatuwa.”

Sai dai bayan wannan furuci na Tinubu, Shugaban Bankin Raya Kasashen Afrika (AfDB), Akinwumi Adesina, ya fitar da wani jawabi da ya ce tattalin arzikin Najeriya ya shuga wani hali.

Yayin wani taron cin abincin cika shekaru 20 da kamfanin Chapel Hill Denham ya shirya a birnin Legas, Adesina ya ce Najeriya ta gaza idan aka kwatanta ta da kasashe irinsu Koriya ta Kudu.

'Hadakar Atiku ta tsorata Tinubu,' Babachir

A baya, mun wallafa cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal, ya bayyana cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana cikin rashin kwanciyar hankali.

Ya bayyana cewa wannan ya biyo bayan fargabar haɗakar ‘yan adawa a karkashin tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El Rufa'i.

Babachir Lawal ya ce hadakar ‘yan adawa ta fara zama babban abin da ke daga hankalin fadar shugaban kasa saboda ganin ta fara karbuwa a tsakanin yan Najeriya kafin 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng