Yadda Abba Ya Canza Rayuwar Kananan Yaran da Ya Gani Suna Barci a Titi a Kano
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaici a kan yadda ya yi kicibis da wasu yara kanana suna barci da misalin 2:00 na dare
- Abin da ya gani ya tayar masa da hankali, inda nan take ya bayar da umarnin a gano iyayen yaran domin jin dalilin barin yaransu a titi
- Bayan gano iyayen yaran, sun bayyana a ofishin Gwamna, an tattauna batutuwa da dama a kan ci gaban ilimin yaran da mataki na gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – A ci gaba da nuna kulawarsa da jinƙai ga marasa galihu, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da iyayen yaran da ya gani suna kwance suna barci a bakin titi da tsakar dare a titin Lodge.

Kara karanta wannan
Faɗan daba: Ɗan siyasa ya haɗa kan matasa da ba su ga maciji a Kano, an samu mafita
Gwamnan ya ci karo da yaran ne da misalin 2:00 na dare yayin da yake yawo don duba aikin ci gaban da gwamnati ke gudanarwa a titin.

Source: Facebook
A sakon da hadimin gwamnan, Ibrahim Adam ya wallafa a shafinsa na Facebook, Injiniya Abba ya nuna matuƙar damuwa da halin da yaran ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa gwamnan ya kuma bayar da umarni a nemo iyayen yaran domin jin dalilin da yasa suka bar su kwana a titi.
Gwamna da iyayen yara masu barci a hanya
A ranar 4 ga Mayu, 2025, iyayen yaran suka gurfana a ofishin Gwamna Abba Kabir Yusuf da ke fadar gwamnatin Kano, kamar yadda ya umurta.
Rahotanni sun ce gwamnan ya karɓe su da hannu biyu, ya saurari bayani daga bakin iyayen kan halin da suka tsinci kansu da kuma dalilin da ya sa yaran suke kwana a waje.

Source: Facebook
Bayan jin matsalarsu, Gwamnan ya bayar da umarni nan take a ba iyayen wadatattun kayan abinci da kuɗi domin su iya yin cefane da kula da lafiyar yaran.
Gwamnan Kano ya taimakawa iyayen yaran
Sakon da hadimin gwamnan ya kara da cewa Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ɗauki nauyin karatun yaran, tare da duk sauran kannensu da ba sa zuwa makaranta.
Wannan, a cewarsa, yana daga cikin manufofin gwamnatin sa na tabbatar da cewa kowane ɗan Kano ya samu ilimi mai nagarta da domin samun rayuwa mai inganci.
Tuni jama’a suka fara yabawa da irin wannan mataki da gwamnan ya ɗauka, tare da bayyana yadda salon mulkin Abba ya tabbatar da tausayinsa kan talakwa.
Ukasha Haruna Sarki Jega ya ce:
"Abba ya chika jagoran tausayin talakawa."
Haruna Isah ya wallfa cewa:
"Lamarin Abba fa saidai kawai mutum ya sallama inyaki bakin ciki da ciwon hassada sukashe mutum."
Sulaiman Nata'ala ya ce:
"Jagora na gari Allah yakara kareka da shairin mahaddasa."
"Kyau a hukunta irin wadannan iyaye"
Shi kuwa wani Abdullahi Jalo ya soki lamarin, ya na ganin kamata ya yi a hukunta iyayen wannan yara, ya rubuta a Facebook:
"Yanzu wani sai yazo yace maka gwamna ya kyauta ya dauke yara daga layi ya kira iyaye ya taimake su.
In dai ba mu fara hukunta iyayen banza ba ba za a daina samun irin wannan matsalar ba.
Iyayen da ya kamata a kama a kulle su ne gwamna ya ke hoto da su. A yi dai mu gani."
Gwamnan Kano ya goyi bayan Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Abba Kabir Yusuf, ya sake bayyana cikakken goyon bayansa da biyayya ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Gwamnan ya jaddada mubaya'arsa ne yayin wata ganawa da ya yi da kansiloli 484 da aka zaba daga kananan hukumomi 44 na jihar a fadar gwamnatin Kano bayan zargin da aka masa.
Injiniya Abba ya jadda cewa duk da i irin zarge-zargen da ake yi a kan Sanata Rabi'u Kwankwaso, ba zai sa su canja akida ko barin tafiyar Kwankwasiyya ba, saboda nagartar da yake da ita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

