"Ki Fito da Hujjoji": An Nemi Sanata Natasha Ta Kawo Karshen Rigimarta da Akpabio

"Ki Fito da Hujjoji": An Nemi Sanata Natasha Ta Kawo Karshen Rigimarta da Akpabio

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ki janye karar da ta shigar kan Akpabio kan zargin cin zarafi, tana cewa shari'a ce za ta warware gaskiya
  • Natasha ta bayyana cewa duk wasu ƙarin hujjoji da za su fito za a gabatar da su ne kawai a lokacin sauraron ƙarar ta hanyar bin doka
  • Sai dai kuma, wani mai sharhi kan siyasa, Ibrahim Jamiu Adamu, ya ce rikicin Natasha da Akpabio ya na tauye hakkin al'ummar Kogi ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi watsi da kiran da ake yi mata na janye ƙarar da ta shigar kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

'Yar majalisar da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta shigar da Akpabio kara dangane da zargin cin zarafi ta ɓangaren jima’i, inda ta ce za ta ci gaba da bin kadin lamarin a gaban kotu.

Kara karanta wannan

Allah mai iko: Dattijuwa ƴar shekara 102 ta karbi Musulunci, an yaba da jajircewarta

Sanata Natasha ta ki amince wa ta janye shari'arta da Akpabio, an nemi ta kawo hujjoji
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, 'yar majalisar Kogi ta Tsakiya. Hoto: Natasha Akpoti
Source: Facebook

Sanata Natasha ta ki amince da bukatar janye karar da ta shigar a cikin wata wasiƙa da ta aikewa Olisa Agbakoba (SAN), lauyan Akpabio, mai ɗauke da kwanan wata 30 ga Afrilu, 2025, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha ta ki yarda ta janye shari'arta da Akpabio

A cikin wasikar, Sanata Natasha ta dage cewa ƙorafinta ya ƙunshi gaskiyar abin da ya faru, kuma za a warware shi ne ta hanyar tsarin shari’a kawai.

'Yar majalisar ta soki ƙoƙarin lauyan Akpabio na neman hujjoji a wajen kotu, tana cewa hakan na nuna rashin fahimtar ainihin yanayin cin zarafi da kuma dokokin shari’a.

Sanatar ta kuma bayyana rashin jin daɗinta kan yadda shugaban majalisar dattawa da ƙoƙarin warware batun a kafofin watsa labarai maimakon bin hanyar doka.

Ta ce irin wannan mataki da Akpabio ke ɗauka ya saba wa ƙa’idojin shari’a, domin yana neman goyon baya daga jama’a alhali shari’ar na gaban kotu.

Kara karanta wannan

'Dillacin kwayoyi': Amurka ta fadi lokacin fitar da bayanan sirri game da Tinubu

Natasha ta bayyana cewa duk wasu ƙarin hujjoji da za su fito za a gabatar da su ne kawai a lokacin sauraron ƙarar ta hanyar bin doka.

Illar rikicin Natasha, Akpabio ga Kogi ta Tsakiya

Ibrahim Jamiu Adamu, wani mai sharhi kan al'amuran siyasa, ya bayyana cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gaza wakiltar mazabarta yadda ya kamata.

A wata tattaunawa da Legit Hausa, Adamu ya ce al’ummar Kogi ta tsakiya na fama da rashin wakilci saboda rikicin Sanata Natasha da shugaban majalisa, Akpabio.

Ya ce bayan dogon nazari, ya fahimci cewa Natasha ba ta fahimci nauyin aikin da aka dora mata na wakiltar jama’a a majalisa ba.

A cewarsa, maimakon ta tsaya kan wakilcin da mutane suka dora mata, sai ta koma yin maganganun neman neman tausayin jama'a kan rigimar da ita ta faro ta tun farko.

Ibrahim Jamiu Adamu ya ce:

"Da irin wannan abin da take ta yi a yanzu, bai kamata a ganta a majalisar dattawa ba, domin wuri ne da yake cike da natsuwa da sanin ya kamata ga mutanen da suka dace.

Kara karanta wannan

'Sun gane kuskurensu,' An bankado shirye shiryen Atiku da Obi a kan zaben 2027

"Da ace za a yi kuturunka nawa a mazabar Kogi ta Tsakiya, ba za a iya samun wasu abubuwan a zo a gani na ci gaba da ta kawo wa wannan yanki ba."

An nemi Natasha ta kawo hujjo don warware rigimar

Dangane da dagewar Sanata Natasha kan ci gaba da shari'a da Akpabio game da zargin neman lalata da ita, Ibrahim Jamiu ya ce ya kamata 'yar majalisar ta hakura, tunda an fara juya mata baya.

A cewar Ibrahim:

"A kwana-kwanan nan kowa ya ga yadda Dr. Sandra Duru wacce aka fi sani da Prof Mbegke ta janye jikinta daga mara mata baya domin yadda ta bankado cewa tana son yin amfani da ita wajen cimma wata manufa da babu daraja a cikinta."

Sai dai, Channels TV ta rahoto cewa, Sanata Natasha ta fito ta karya ta wannan ikirari na Dr. Sandra, inda ta ce ba ta yi wa 'yar gwagwarmayar tayin N200m don laka wa Akpabio sharri ba.

Duk da karyatawar da Natasha ta yi, Ibrahim Jamiu ya nuna cewa abubuwan da ke faruwa a wannan badakalar, na bukatar 'yar majalisar ta kawo hujjoji kawai don kare kanta.

"Natasha ki kawo hujja kawai idan akwai. Ki daina wasa da hankalin jama’a, ya isa haka" a cewar Ibrahim Jamiu Adam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com