Gwamnatin Kano Ta Yi Wa Baffa Bichi Martani mai Zafi, Ta Fadi Dalilin Korarsa
- Gwamnatin jihar Kano ta kasa kawar da kai daga zarge-zargen da Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya yi a kanta a 'yan kwanakin nan
- Kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida na jihar, ya bayyana zarge-zargen a matsayin wata ƙiyayya ta siyasa
- Ibrahim Garba Waiya ya ƙalubalanci tsohon sakataren gwamnatin Kano da ya fito ya gabatar da hujjojinsa kan zarge-zargen da ya yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ta mayar da martani mai zafi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Baffa Bichi, ya yi.
Gwamnatin ta bayyana cewa cire shi daga muƙaminsa ba wai saboda rashin lafiyarsa kawai aka yi ba, kamar yadda aka sanar a baya.

Source: Facebook
Kwamishinan watsa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Ibrahim Garba Waiya, ya yi martanin a ranar Juma'a, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Baffa Bichi ya zargi gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da aikata rashawa, yana mai cewa ta fi gwamnatin da ta gabata ƙarƙashin Abdullahi Ganduje muni.
Me gwamnatin Kano ta ce kan zarge-zargen Baffa?
Kwamishinan ya bayyana zarge-zargen a matsayin masu ɗauke da ƙiyayya ta siyasa, marasa tushe, kuma ƙoƙari ne na yaudarar jama’a.
Ibrahim Waiya ya ƙalubalanci tsohon SSG ɗin da ya gabatar da hujjojin da ke tabbatar da iƙirarin nasa.
“Zargin da ya yi abin takaici ne kuma yana da niyyar ɓata suna. Wannan gwamnati na da cikakken tsari na gaskiya, riƙon amana da hidima ga jama’a."
"Kwatanta ta da gwamnatin da ta gabata rashin adalci ne kuma ci gaba ne da cutar da al’ummar Kano."
“Idan da gaske yana da hujja kan rashawa, muna ƙalubalantar sa da ya fito fili ya gabatar da su. Zarge-zarge marasa tushe ba za su hana wannan gwamnati cigaba da aikinta ba."

Kara karanta wannan
Bayan korar shi, Baffa Bichi ya ce Abba ya fi Ganduje barna a gwamnatin jihar Kano
- Ibrahim Waiya

Source: Facebook
Meyasa aka kori Abdullahi Baffa Bichi
Kwamishinan ya kuma fayyace dalilan da suka sa aka sallami Abba Bichi daga gwamnati.
“Mun ɓoye ainihin dalilin da ya sa aka kore shi, muka ce matsalar rashin lafiya ne, saboda mutuntawa. Amma ya kamata a sani cewa cire shi ba kawai saboda rashin lafiya aka yi ba."
"Duba da irin yadda yake fitar da maganganu, ina ba da shawara da ya nemi taimakon likita. Lafiyarsa ce ya kamata ta fi damunsa a yanzu."
- Ibrahim Waiya
Gwamnatin jihar ta nanata ƙudurinta na kyakkyawan shugabanci tare da roƙon jama’a da su yi watsi da waɗannan zarge-zargen marasa tushe, waɗanɗa ta ce an yi su ne don karkatar da hankali daga ainihin aikin raya jihar.
NLC ta goyi bayan tazarcen Gwamna Abba
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) reshen jihar Kano ta gamsu da kamun ludayin mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan
Atiku ko Obi?: El Rufa'i ya yi magana kan tsayar da 'dan takaran 'yan adawa a 2027
Ƙungiyar ta NLC ta bayyana goyon bayan ta ga Gwamna Abba Kabir Yusuf kan ya zarce mulkin Kano a wa'adi na biyu.
NLC ta yabawa gwamnan kan irin kulawa da maida hankali kan jin daɗin ma'aikata da ƴan fansho da yake yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
