Bugaje: Tsohon Dan Majalisa Ya Yi Wa Gwamnatin Tinubu Wankin Babban Bargo
- Tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya, Usman Bugaje ya nuna rashin gamsuwarsa da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Usman Bugaje ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kasa magance matsala ko guda ɗaya daga cikin waɗanda ta zo ta tarar a ƙasar na
- Tsohon ɗan majalisar Jibia/Kaita ya bayyana cewa gwamnatin ta fi maida hankali kan siyasa maimakon sauke nauyin da aka ɗora mata
- Bugaje wanda ya taba aiki a Aso Rock ya ce bayan shekara biyu da kafuwarta, har yanzu bai ga wani abu da ta tsinanawa ƴan Najeriya ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan majalisar wakilai, Usman Bugaje, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Usman Bugaje ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta kasa magance matsalolin da ta gada daga gwamnatin da ta gabata.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi karatun ta natsu, ya gano matsalar da ya kamata a magance a Najeriya

Source: Facebook
Usman Bugaje ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa a shirin 'Daily Politics' na tashar Trust Tv a ranar Alhamis, 30 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me tsohon ɗan majalisa ya ce kan Tinubu?
Tsohon ɗan majalisar ya ce gwamnatin Tinubu na bai wa siyasa muhimmanci fiye da mulki a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke buƙatar a kawo sauyi mai gamsarwa.
“Akwai koke-koke ba kawai a Arewa ba, har ma a Legas inda shugaban ƙasa ya fito."
“Ba adalci ba ne ka fara yin siyasa alhali ba ka cika alƙawuran da ka ɗauka ba. Lokacin siyasa zai zo, amma yanzu lokaci ne na aiwatar da ayyuka."
-.Usman Bugaje
Bugaje ya ce Tinubu bai taɓuka komai ba
Bugaje ya nuna cewa gwamnatin Tinubu ba ta cika alƙawurran da ta ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 ba.
Ya ce har yanzu gwamnatin ba ta magance manyan matsalolin ƙasa ba, ciki har da rashin tsaro, talauci, da ci gaban ɗan Adam, waɗanda a cewarsa su ne ginshikan cigaban ƙasar.

Source: Facebook
“Wannan shi ne abin da ake magana a kai. Maimakon kashe kudi a siyasa, kamar sanya hotuna a manyan alluna a ko’ina da gudanar da kamfe, ya fi dacewa a maida hankali kan aikin da aka zaɓe ka domin yi."
“Wannan ita ce shekara ta biyu ko ƙarshen shekara ta biyu, amma babu wani gagarumin abin da za a iya nunawa a ce an cimma."
“Gwamnatin ta kasa ta kuma gaza wajen magance kowanne daga cikin matsalolin da ta tarar.”
“Ban iya tuna wata matsala guda ɗaya da wannan gwamnati ta warware tun daga lokacin da ta hau mulki"
- Usman Bugaje
Tinubu ya kasa yin kataɓus
Muhammad Auwal ya shaidawa Legit Hausa cewa gwamnatin Bola Tinubu ƙara lalata abubuwa ta yi a Najeriya.
"Dole zan yarda da kalaman da Usman Bugaje ya yi a kan gwamnatin Tinubu. Har yanzu ban ga wata matsala guda ɗaya da ta magance ba a ƙasar nan."

Kara karanta wannan
"Ɗan Arewa kaɗai," Dele Momodu ya faɗi wanda zai iya kayar da Shugaba Tinubu a 2027
"Tsaro ya ƙara taɓarɓarewa, ba wutar lantarki, talauci ya yi wa mutane yawa sannan babu alamun samun sauƙi a nan kusa."
- Muhammad Auwal
Tinubu ya shawarci gwamnoni
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya koma mai ba da shawara ga gwamnonin Najeriya kan masu sukarsu.
Shugaban ƙasan ya buƙaci gwamnonin da su yi kunnen uwar shegu da masu sukar ayyukan da suke gudanarwa a jihohinsu.
Ya buƙace su da su maida hankali wajen sauke nauyin da ke kansu ba tare da sun bari wasu sun karkatar musu da hankali ba.
Shugaban ƙasan ya kuma buƙace da su riƙa duba buƙatun jama'a a cikin shirye-shiryen da suke aiwatarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
