Rigimar Sarauta Ta Dawo Ɗanya, Jami'an Tsaro Sun Kulle Gidan Galadiman Kano

Rigimar Sarauta Ta Dawo Ɗanya, Jami'an Tsaro Sun Kulle Gidan Galadiman Kano

  • Rundunar ‘yan sanda ta mamaye gidan Galadiman Kano da ke Galadanci, Gwale, bayan naɗa Galadima biyu da aka yi a ranar Juma'a
  • Muhammadu Sanusi II ya nada Munir Sanusi Bayero a Gidan Rumfa, yayin da Aminu Ado Bayero ya nada Sanusi Ado Bayero a Nasarawa
  • Iyalin gidan Galadanci sun ce ba su da hannu a rikicin, amma suna cikin damuwa kan yadda siyasa ke rushe musu zumunci da al’ada

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Ana cikin rudani a masarautar Kano bayan jami’an tsaro sun kulle gidan Galadiman Kano da ke Galadanci a karamar hukumar Gwale.

Wannan al’amari da ya faru tun daren Alhamis ya tsananta rikicin masarautar da ya dabaibaye birnin Kano tun da dadewa.

Jami'an tsaro sun mamaye gidan Galadima a Kano
Bayan nadin Galadima a Kano, jami'an tsaro sun mamaye gidan a Gwale. Hoto: Sanusi II Dynasty, Masarautar Kano.
Source: Twitter

Gidan da aka kulle yana da tarihi a matsayin matsugunin Galadima, wanda shi ne muƙami mafi girma a masarautar Kano, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Kwankwaso ya hadu da Sanata Barau Jibrin a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Musabbabin kulle gidan Galadiman Kano

Wannan matakin tsaro ya biyo bayan nadin Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin Galadiman Kano daga Sarki Muhammadu Sanusi II.

Nadin ya kasance wani bangare na jerin nadin mukamai da Muhammadu Sanusi II ya yi a babban fadar Gidan Rumfa.

Cikin wadanda aka nada akwai Alhaji Kabir Tijjani Hashim a matsayin Wamban Kano da Adam Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano.

A wurin bikin, Sanusi II ya bukaci sababbin masu mukamai su nuna kaskantar da kai da shugabanci da sadaukar da kai ga al’umma.

Ya ce:

“An zaɓe ku bisa tarihin ku da na iyalanku. Ku ci gaba da bin sawun kakanninku."

Amma bayan sa’o’i kadan, Aminu Ado Bayero ya gudanar da nasa nadin Galadima a fadar Nasarawa, inda ya nada dan uwansa Sanusi Ado Bayero.

Jami'an tsaro sun kulle gidan Galadima a Kano
Jami'an tsaro sun mamaye gidan Galadima a Kano bayan nadin muƙamin har guda 2. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Masarautar Kano, Nigeria Police Force.
Source: UGC

Iyalan gidan Galadima sun yi magana

Jami’an tsaro da ke zagaye da gidan Galadima sun bar al’ummar Galadanci cikin rudani, musamman iyalan da rikicin ya raba gida biyu.

Kara karanta wannan

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta dare gida 2, an samu hatsaniya kan Seyi Tinubu

“Wannan duk siyasa ce, dukkan Galadiman ’ya’yanmu ne. Munir ya taso a nan, da ba domin ’yan sanda ba, da mun tarbe shi."

- Cewar wani dan gida.

Wata mace daga gidan, da ta bukaci a sakaya sunanta, ta bayyana damuwa da yadda rikicin masarauta ke tarwatsa danginsu, cewar Punch.

Ta ce:

“Gaskiya ba mu goyon bayan kowa, muna cikin bakin ciki. Har shugaban APC na jiha daga gidanmu ne, shi ma ba ya jin dadi."

An samu rahoton cewa Sanusi II ya bayar da umarnin gyaran gidan Galadima domin Munir Sanusi ya koma ciki bisa al’adar masarauta.

Masu goyon bayan Sanusi na ganin kullen gidan a matsayin katsalandan cikin harkokin masarauta da kuma siyasa ba tsaro ba.

Galadiman Kano: An jibge jami'an tsaro a Kano

Kun ji cewa rahotanni sun ce tun daga daren Juma'a, jami’an tsaro su ka mamaye kofar gidan Galadiman Kano da ke unguwar Galadanci, yayin da ake shirin nadin sabon Galadima.

Wannan na zuwa ne a lokacin da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ke shirin nada Munir Sanusi a matsayin sabon Galadima bayan rasuwar Abbas Sanusi.

Haka kuma Sakataren yada labaran fadar Nasarawa ya tabbatar da cewa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero yana nada Sanusi Ado Bayero kan sarautar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.