Ministar Tinubu Ta Yi Babban Rashi, Allah Ya Karɓi Ran Mahaifin Dr. Mariya

Ministar Tinubu Ta Yi Babban Rashi, Allah Ya Karɓi Ran Mahaifin Dr. Mariya

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya miƙa sakon ta'aziyya bisa rasuwar mahaifin abokiyar aikinsa, Dr. Mariya Mahmoud
  • An ruwaito cewa mahaifin ƙaramar ministar harkokin birnin Abuja, Alhaji Sani Baban Koko ya rasu yana da shekara 74 a duniya
  • Wike ya bayyana cewa duk da bai taɓa haɗuwa da mahaifin Dr. Mariya ba, ya san cewa mutumin kirki ne, ya yi addu'ar Allah jiƙan sa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Alhaji Sani Baban Koko, mahaifin ƙaramar ministar harkokin babban birnin tarayya Abuja, Hajiya Mariya Mahmoud ya riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun nuna cewa mahaifin Dr. Mariya, ƴar asalin jihar Kano ya rasu yana da shekaru 74 a duniya.

Dr. Mariya Mahmoud.
Ministan Abuja ya yi ta'aziyyar rasuwar mahaifin Dr. Mariya Hoto: AcresalNigeria
Source: Twitter

Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya yi jimami da ta'aziyya ga ƙaramar ministar bisa rasuwar mahaifinta, Alhaji Sani Baban Koko, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Miyarsa yake gyarawa,' Wike ya soki masoyin Atiku kan neman maido mulki Arewa

Nyesom Wike ya yi alhinin rasuwar mahaifin minista

Wike ya yi alhinin rashin mahaifin abokiyar aikinsa a wata sanarwa da hadiminsa na musamman kan harkokin sadarwa, Lere Olayinka, ya fitar a ranar Laraba,

Ministan ya yi addu’ar samun rahama ga marigayin tare da rokon Allah Ya bai wa iyalansa haƙurin jure rashinsa.

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya ce duk da bai taɓa haɗuwa da mahaifin Dr. Mariya ba amma ganin irin tarbiyyar da ya ƴarsa ya nuna cewa shi mutumin kirki ne.

Wike ya miƙa sakon ta'aziyya ga Dr. Mariya

“Na shiga alhini da jimami a zucuyata a lokacin da na ji labarin rasuwar mahaifinki (Dr. Mariya Mahmoud), Alhaji Sani Baban Koko.
“Ko da yake ban samu damar haɗuwa da Alhaji Sani Baban Koko ba a rayuwarsa, masu iya magana na cewa za a iya gane halin mutum daga ingancin da halayen ƴaƴansa.
“Idan aka yi la’akari da halayen Dr. Mahmoud Mariya, daya daga cikin ‘ya’yansa, zan iya cewa Baba mutum ne mai nagarta kuma mutumin kirki.”

Kara karanta wannan

Ayyukan gwamna sun ja ra'ayin Ɗan Majalisar Tarayya, ya sauya sheƙa zuwa PDP

- In ji Nyesom Wike.

Ministan ya ƙara da cewa rasuwar mahaifi abu ne mai matuƙar zafi da ƙuna, inda ya buƙaci iyalai da ƴan uwan marigayin su ƙara hakuri kuma su kwantar da hankulansu.

Dr. Mariya da Wike.
Wike ya yi addu'ar Allah jiƙan mahaifin Dr. Mariya Hoto: @officialFCTA
Source: Twitter

Addu'ar da Wike ya yi wa mahaifin minista

Wike ya ƙara da cewa:

"Rasuwar uba abu ne mai matukar zafi, musamman idan aka yi la’akari da cewa ya rasu yana da shekaru 74.
"Amma ya kamata iyalan Baban Koko su kwantar da hankalinsu kuma su tuna cewa mutuwa dole ce ga kowa.
“Don haka ina addu’a Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) cikin rahamarSa, ya sa marigayi Alhaji Sani Baban Koko a Aljannatul Firdaus, ya kuma ba ku hakurin jure wannan rashi.”

Mahaifiyar Sheikh Asadus Sunnah ta rasu

A wani labarin, kun ji cewa Allah ya yi wa mahaifiyar babban malamin nan, Sheikh Musa Yusuf Asadus Sunnah rasuwa.

Rahotanni sun nuna cewa tuni aka gudanar da sallar jana'izar marigayiyar a masallacin Juma'ah na Musabaqah da ke Unguwar Kinkinau a Kaduna.

Mutane da dama sun yi alhini tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar musamman Asadus Sunnah, wanda yana ɗaya daga cikin manyan malaman addini.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262