Delta: Hadimin Gwamna Ya Fusata, Ya Yi Murabus daga Muƙaminsa kan Matsalar Tsaro

Delta: Hadimin Gwamna Ya Fusata, Ya Yi Murabus daga Muƙaminsa kan Matsalar Tsaro

  • Hadimin Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta, Harrison Gwamnishu, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda matsalar tsaro
  • Harrison Gwamnishu ya ce ya miƙa ƙorafe-ƙorafe tare da shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro amma gwamna ya yi watsi da su
  • Ya ce a matsayinsa na ɗan gwagwarmaya mai kokarin kare haƙkin al'umma, ya yi murabus ne domin jawo hankalin gwamnan Delta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Mai ba Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, shawara ta musamman kan Kungiyoyin Fararen Hula da Matasa, Harrison Gwamnishu, ya yi murabus.

Hadimin gwamnan ya yi murabus daga muƙaminsa ne saboda taɓarbarewar tsaro a jihar Delta wanda ya yi zargin gwamnan ya ƙi magancewa.

Gwamnan Delta da tsohon hadiminsa.
Hadimin gwamnan Delta. Harrison Gwamnishu, ya yi murabus Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori, Harrison Gwamnishu
Source: Facebook

Harrison Gwamnishu ya tabbatar da hakan ne cikin wasikar murabus da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai ɗauke da kwanan watan 25 ga Afrilu 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnan Delta ya fadi babban jigon PDP da zai koma jam'iyyar APC

Me yasa Hadimin gwamnan ya yi murabus?

Gwamnishu ya bayyana cewa ƙaruwar matsalar tsaro a jihar Delta ce ta tilasta masa ɗaukar wannan mataki.

Ya ce duk da kokarinsa na fadakar da Gwamna Sheriff ta hanyar kai masa ƙorafi da gabatar da tsare-tsare don magance lamarin, amma ya yi watsi da su.

“Duk da sakonni da kira da takardun shawarwarin mafita da nake aikawa domin fuskantar wadannan matsaloli na tsaro, duk an yi watsi da su.
"Na fahimci cewa ba a son karbar shawarar da za ta kawo mafita a wannan gwamnati. Kuma matsayin shugaban kungiyoyin kare hakkin jama’a, na karbi wannan mukami da niyyar kare al’umma.
"Amma yadda matsalar tsaro ke kara tsananta da rashin daukar matakin da ya dace ya hana ni cika aikina. Don haka na yi murabus domin jawo hankali kan bukatar daukar matakin gaggawa don kare al’umma.”

- Harrison Gwamnishu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Okowa ya bayyana lokacin da Atiku zai fice daga jam'iyyar PDP

Da aka tuntube shi, Gwamnishu ya ce “garkuwa da mutane da fashi da makami," su ne manyan matsalolin tsaro da ya kai ƙorafi ga gwamna, amma ba a dauki mataki ba.

Gwamnan Delta.
Gwamnatin Delta ta ce hadimin gwamna da ya yi murabus bai san komai ba Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori
Source: Facebook

Wane mataki gwamnan Delta ya ɗauka?

Sai dai kwamishinan ayyuka na jihar Delta, Charles Aniagwu, ya ce Gwamnishu karamin jami’i ne a gwamnati kuma bai san abubuwan da ake yi wajen shawo kan matsalolin tsaro ba.

Ya ce:

“Matsayin aikinsa bai kai inda zai san abin da ke faruwa a fannin tsaro ba. Bai ma san cewa gwamnatin jihar ta raba motocin sintiri sama da 60 ga jami’an tsaro ba."
“Idan har matsalar tsaro ce ta tilasta masa yin murabus, me yasa sauran hadiman gwamnati da suke a yankunan da ake fama da matsaloli ba su yi murabus ba?”

Gwamnan Delta ya fara yi wa APC aiki

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya ce yana sa ran nan ba da jimawa zai tarbi tsohon gwamnan jihar, James Ibori, a jam’iyyar APC.

Wannan kalamai na zuwa ne bayan gwamnan tare da dukkan shugabannin PDP a Delta sun tattara kayansu sun koma APC mai mulkin Najeriya.

Gwamna Oborevwori ya bayyana cewa gidan siyasar da James Ibori ya kafa ya tarwatse, yana mai jaddada bukatar haɗa kai don ciyar da Delta gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262