Giwa: Gobara Ta Tashi a Rumbun Makaman Sojojin Najeriya a Maiduguri
- Rundunar Operation Hadin Kai ta sanar cewa wuta ta tashi a rumbun ajiyar makamai a jihar Borno saboda zafi
- Boma bomai sun tashi a ma’ajiyar makamai da ke barikin Giwa a Maiduguri, amma ba a samu asarar rayuka ba
- Rahotanni sun nuna hukumar kashe gobara ta jihar Borno da jami’an tsaro sun dakile lamarin cikin kankanin lokaci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya da ke aiki a karkashin Operation Hadin Kai ta sanar da cewa an samu tashin wuta a barikin Giwa da ke Maiduguri.
Rudunar ta bayyana cewa hadari aka samu saboda tsananin zafi ba wani hari aka kai ba kamar yadda ake yadawa.

Source: Twitter
Legit ta samo bayanan da rundunar ta yi ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X bayan shawo kan wutar.

Kara karanta wannan
Bayan fashewar wasu makamai a barikin sojoji, an ji halin da ake ciki a Maiduguri
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce an shawo kan lamarin cikin gaggawa da hadin gwiwar hukumar kashe gobara ta jihar Borno da sauran hukumomin tsaro.
Kakakin rundunar, Kyaftin Reuben Kovangiya ne ya fitar da sanarwar, inda ya bukaci jama’a da su kwantar da hankalinsu su kuma yi watsi da jita-jitar cewa hari aka kai wa Maiduguri.
Zafi ya haddasa fashewar makamai a Borno
A cewar sanarwar, makaman sun kama da wuta ne sakamakon matsanancin zafin rana da ake fama da shi a birnin Maiduguri.
Wannan na zuwa a daidai lokacin da yanayin zafi ke kara tsananta a sassa da dama na Arewa maso Gabas.
Bayan faruwar lamarin, an hanzarta kiran jami’an kashe gobara na jihar Borno da wasu daga cikin jami’an tsaro da ke da motocin kashe gobara, inda suka kai dauki cikin gaggawa.
An tura sojoji don hana ‘yan daba cin moriya
Rundunar ta bayyana cewa an tura dakarun Operation Hadin Kai zuwa wuraren da fashewar ta shafa domin hana wasu bata-gari amfani da wannan lamari wajen tada hankali ko yin fashi.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa babu wani hari da aka kai wa birnin Maiduguri, kuma komai na tafiya daidai a yanzu haka.
Kyaftin Kovangiya ya bukaci jama’ar Maiduguri da su kwantar da hankalinsu, su kuma ci gaba da bayar da hadin kai da ba da bayanai idan suka lura da wani abu mai barazana ga tsaro.
Haka zalika, kakakin 'yan sandan jihar Borno, Nahum Kenneth Daso ya wallafa a X cewa an shawo kan lamarin kuma komai ya fara tafiya lafiya a halin yanzu.
Legit ta tattauna da mazaunin Maiduguri
Wani mazaunin Maiduguri, Ali Bulama ya zantawa Legit cewa sun shiga firgici a lokacin da suka fara jin fashe fashen.
Ali Bulama ya ce:
"Hankalin mutane ya tashi sosai, musamman da ake cewa Boko Haram suna shirin dawowa da karfinsu.
"Mun samu sauki da muka ji cewa gobara aka samu. Allah ya kiyaye na gaba."
'Yan ta'adda sun kai hari gidan basarake a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da manyan makamai sun kai hari gidan wani basarake a jihar Kaduna.
Rahotanni sun tabbatar da cewa 'yan bindigar sun sace matar basaraken da wata 'yar shi sun tafi da su cikin daji.
Wani daga cikin mutanen garin ya rasa ran shi yayin da aka hada wata tawaga cikin daji domin ceto matan daga hannun 'yan ta'addan.
Asali: Legit.ng

