Gwamna Buni Ya Lissafo Abubuwa 2 da Suka Hana Rikicin Boko Haram Karewa

Gwamna Buni Ya Lissafo Abubuwa 2 da Suka Hana Rikicin Boko Haram Karewa

  • Mai girma Gwamnan jihar Borno, Mai Mala Buni, ya gano matsalolin da suke ƙara rura wutar rikicin ƴan ta'addan Boko Haram
  • Mai Mala Buni ya bayyana talauci da jahilci a tsakanin matasa a yankin Arewa maso Yamma na rura wutar rikicin Boko Haram
  • Gwamnan ya yi nuni da cewa yana da matuƙar muhimmanci a magance matsalolin domin a samu damar kawo ƙarshen rikicin
  • Tsohon shugaban na APC ya ce rashin magance matsalolin zai ci gaba da yin barazana ga zaman lafiya da ci gaban Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya yi magana kan rikicin Boko Haram wanda ya ƙi ya ci ya ƙi cinyewa.

Gwamna Mai Mala Buni ya danganta tashin hankalin Boko Haram da talauci da kuma rashin ilimi a tsakanin matasa a yankin Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Bayan komawa APC, Okowa ya fadi nadamarsa kan takara da Atiku a 2023

Gwamna Mai Mala Buni
Gwamna Buni ya ce talauci da jahilci na taka rawa a rikicin Boko Haram Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana hakan ne ta bakin sakataren gwamnatin jihar Yobe, Baba Malam Wali, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Ya yi kalaman ne tayin wata ziyara da ɗaliban cibiyar nazarin harkokin tsaro ta ƙasa (NISS) suka kai jihar Yobe a ranar Litinin, 28 ga watan Afirilun 2025.

Gwamna Buni ya magantu kan Boko Haram

Gwamna Mai Mala Buni ya bayyana cewa jahilci da talauci sun taka rawa matuƙa wajen ƙara ƙarfin ayyukan ta’addanci a wannan yankin na Arewa maso Gabas.

"Rashin ilimi da talauci sun taka muhimmiyar rawa wajen sake bayyanar ƙungiyar Boko Haram."
"Yana da matuƙar muhimmanci mu ci gaba da aiki don shawo kan waɗannan matsaloli."

- Gwamna Mai Mala Buni

Ya jaddada cewa dole ne a magance tushen matsalolin domin a samu nasarar daƙile ta’addanci, yana mai gargaɗin cewa gazawa a wannan fannin zai ci gaba da haifar da barazana ga zaman lafiya da ci gaba.

Kara karanta wannan

Shirin Bola Tinubu da Wike kan Gwamna Fubara da aka dakatar

Gwamnatin Yobe na ƙoƙarin yaƙi da talauci

Gwamnan ya sake tabbatar da ƙudirin hwamnatin Yobe na yaƙi da talauci da jahilci ta hanyar shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziƙi, sake gina makarantun da suka lalace, da kuma ɗaukar sababbin malamai domin inganta harkar ilimi a jihar.

Gwamna Buni
Gwamna Buni ya ce akwai bukatar magance Boko Haram Hoto: Hon. Mai Mala Buni
Source: Facebook

Tun da farko, shugaban tawagar NISS, Alhaji Ibrahim Abdullahi Yar’adua, ya bayyana cewa ziyarar na da nufin nazarin yanayin tsaro na jihar da kuma gano kyawawan hanyoyin da za a bi domin su taimaka wajen tsara manufofin tsaron ƙasa.

Ya ce wannan aiki zai samar da wani cikakken rahoto da za a yi amfani da shi wajen tsara manufofin gwamnati kan harkokin tsaro a matakin ƙasa.

Ƴan ta'adda sun lalata gada a Yobe

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'adda ake zargin mayaƙan ƙungiyar ISWAP ne sun lalata wata gada a jihar Yobe.

Ƴan ta'adan na ISWAP sun tarwatsa gadar wacce ta haɗa Ngurbuwa da Goniri a ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa tsagerun sun lalata gadar ne ta hanyar amfani da wani bam a harin da suka kai cikin dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng