Farfesa Usman Yusuf Ya Taso Tinubu a Gaba, Ya Fadi Shirinsa kan Masu Sukar Gwamnati
- Tsohon shugaban hukumar NHIS, Farfesa Usman Yusuf ya yi magana kan kamun da hukumar EFCC ta yi masa
- Farfesa Usman Yusuf ya bayyana cewa kamun da aka yi masa na da nasaba da ƙoƙarin gwamnatin Bola Tinubu na rufe bakin masu sukarta
- Tsohon shugaban na NHIS ya bayyana cewa ba zai ji tsoro ba domin shi ba irin mutanen da ake rufewa baki ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban hukumar kula da inshorar lafiya ta ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu.
Farfesa Usman Yusuf ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da danne ƴancin masu sukar gwamnati da kuma ƙoƙarin rufe musu baki.

Source: Facebook
Tsohon shugaban na NHIS ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise Tv a ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Usman Yusuf ya magantu kan cafke shi
Farfesa Usman Yusuf ya yi zargin cewa kama shi da tsarewar da aka yi masa, an shirya su ne da gangan domin tsoratar da shi da kuma raunana azamarsa wajen sukar manufofin gwamnati.
A watan Fabrairu, hukumar EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf gaban kotu bisa zargin aikata damfara.
Ya musanta laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban mai Shari'a Chinyere Nwecheonwu ta babbar kotun babban birnin tarayya Abuja.
Me Usman Yusuf ya ce kan Tinubu
Tsohon shugaban na NHIS ya bayyana lokacin da ya kwashe a gidan yarin Kuje a matsayin wani lokaci na hutawa, yin addu'a da kuma tunani, yana mai jaddada cewa hakan ya ƙara masa karfin gwiwa.
"Samun beli haƙƙine da kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada ga kowanne wanda ake tuhuma, sai dai idan ana tuhumarsa da laifin kisa ko ta’addanci, kuma batuna bai shafi irin waɗannan laifuka ba."
“Wannan gwamnati da gangan ta hana ni beli domin ta girgiza ni. Na kwashe kwana shida a hannun EFCC sannan na shafe kwana 24 a gidan yari na Kuje, duk ƙoƙari ne na rufe mini baki. Amma ni ba mutum ba ne wanda za a iya hana yin magana."
“Dukkan manufar ita ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ƙoƙarin hana duk wani nau'in adawa.”
Farfesa Usman Yusuf

Source: UGC
"Wannan kuwa na fitowa ne daga shugaban da shi kansa tsohon ɗan NADECO ne, wanda ya taɓa yin faɗa saboda mulkin soja, ya gudu har waje domin tsira."
"Yin suka ga gwamnati a cikin dimokuradiyya haƙƙi ne na kowanne ɗan kasa. Amma yanzu, Shugaba Tinubu yana ƙoƙarin murƙushe masu adawa da gwamnati tare da maida Najeriya zuwa ƙasa mai jam’iyya ɗaya ta mulki da danniya. Ba za mu bari hakan ya faru ba."
- Farfesa Usman Yusuf
Shirin Tinubu kan dawo da Fubara
A wani labarin kima, kun ji cewa tsohon shugaban tsagerun Niger Delta, Government Okpemubolo wanda aka fi sani da Tompolo ya yi magana kan dawo da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Tompolo ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu da Nyesom Wike na ƙoƙarin ganin an maida gwamnan kan kujerarsa.
Ya nuna cewa za a samu maslaha a tsakanin ɓangarorin da rikicin siyasar jihar Rivers da ya daɗe yana ci ya shafa.
Asali: Legit.ng

