El Rufai Ya Sake Caccakar Tinubu, Ya Fadi Yadda Ya Lalata Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sake nuna rashin gamsuwarsa kan kamun ludayin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- El-Rufai ya zargi shugaban ƙasan da nuna son kai waken rabon muƙamai da kuma mayar da Najeriya baya tun da ya hau kan kujerar mulki
- Hakazalika ya zargi Shugaba Tinubu da taɓarɓarar da tattalin arziƙin Najeriya da kuma kaucewa manufofin da suka kafa jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake taso gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaba.
Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da rashin ƙwarewa, nuna son kai da kuma cin amanar manufofin da suka kafa jam’iyyar APC.

Asali: Twitter
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar DW Hausa a jihar Katsina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me El-Rufai ya ce kan gwamnatin Tinubu?
El-Rufai, wanda kwanan nan ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP, ya yi zargin cewa Najeriya na ƙara komawa baya tun daga lokacin da Tinubu ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
A cewarsa, halin da ƙasar ke ciki yanzu ya fi muni fiye da yadda take a lokacin gwamnatocin baya, ta fuskar rashin tsaro, tattalin arziƙi da shugabanci.
Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da kabilanci, son kai da rashin tausayi da halin da talakawan Najeriya ke ciki.
“Tun da Tinubu ya hau mulki a matsayin shugaban ƙasa, Najeriya ta fara komawa baya. Rashin tsaro ya ƙaru, tattalin arziƙi ya mutu, attajirai sun tsiyace sannan ga ƙabilanci wurjanjan."
"Mutum ya tashi duk wanda zai ba muƙami sai dai wanda ya sani ne ko ɗan ƙabilarsa. Za su iya musanta hakan, amma ƴan Najeriya ba shashahu ba ne."
-.Nasir El-Rufai
El-Rufai ya kare kansa kan barin APC
Dangane da damuwar cewa tafiyarsa da SDP na iya yin ƙarshe kamar irin ƙawancen da ya yi da APC a baya, El-Rufai ya jaddada cewa APC ce ta kauce daga manufofinta da aka gina ta a kai, ba shi ba.

Asali: Twitter
“Ni ban bar APC ba, jam’iyyar ce ta bar ni. Tun da Bola Tinubu ya zama shugaban ƙasa, ƙasar ta fara komawa baya."
"Mun sha faɗa musu cewa abin da suke yi ba daidai ba ne, amma kullum suna nuna kamar babu wanda zai iya gaya musu gaskiya.”
“Ko da suna musanta zargin nuna son kai da fifita wata ƙabila, mutane ba makafi ba ne kuma ba wawaye ba ne. Idan mutane suka ga sunaye, suna gane daga inda mutum ya fito."
- Nasir El-Rufai
An gargaɗi ƴan Najeriya game da El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiyar matasan Arewa mai suna NCM ta nuna alamar tambaya kan ƙawancen da Nasir El-Rufai yake yi da Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan
'Ciwon ido': Jigon PDP ya faɗi mutane 2 da za su zama barazana ga ƴan adawa a 2027
Ƙungiyar ta nuna shakku kan irin girmamawar da El-Rufai ke yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasan a yanzu.
Ta ja kunnen ƴan Najeriya kan ka da su ɗauki ɗasawar da El-Rufai ke yi da Atiku a matsayin wani sulhu na gaskiya, face wani yunƙurinsa na cimma wata manufa ta siyasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng