'Dan Majalisa Ya Rikita Matasan Borno da Aiki a Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya
- Ɗan majalisar wakilai daga Borno, Usman Zanna, ya sake ba wasu matasa ayyukan yi a ma'aikatun gwamnatin tarayya domin tallafawa mazabarsa
- Wani yaronsa, Yahaya Sa’idu ya bayyana cewa a ranar Litinin 14 ga Afrilu, 2025, Hon. Zanna ya taimaka wa wasu matasa biyu da sababbin ayyuka
- Yahaya ya kara da cewa dan majalisar ya ba matasa fiye da 300 guraben aikin yi tun bayan shigarsa majalisa, wanda zama garkuwa ga al’ummarsa
- Abdullahi Bukar, wanda ya samu aiki a hukumar NDLEA a shekarar 2023, ya ce ya san da sababbin wadanda aka ba aiki a jiya daga mazabar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - 'Dan majalisar tarayya daga Borno ya sake gwangwaje matasa da ayyukan yi a jihar da ke Arewacin Najeriya.
Hon. Usman Zanna da ke wakilar mazabar Kaga/Magumeri/Gubio ya kuma ba wasu matasa aiki a ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Asali: Facebook
Yadda ɗan majalisa ya ba matasa aiki
Daya daga cikin yaransa, Yahaya Sa'idu shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Talata 15 ga watan Afrilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yahaya Sa'idu ya ce dan majalisar ya zama bango ga al'ummar mazabarsa saboda ayyukan alheri da yake yi.
Ya ce ko a yau (Litinin) 14 ga watan Afrilun 2025, Hon. Zanna ya ba wasu matasa guda biyu aiki wadanda suka fito daga mazabar dan majalisar.
Har ila yau ya ce wannan ba shi ne karon farko ba da dan majalisar ke rabawa matasa aikin yi a mazabarsa.
Matashin ya ce akalla Hon. Zanna ya ba mutane sama da 300 aikin yi daga zuwansa majalisa zuwa yau.

Asali: Facebook
Tattaunawar Legit Hausa da matashi da ya samu aiki
Wakilin Legit Hausa ta yi magana da wani daga cikin wadanda dan majalisar ya ba aiki a shekarar 2023 da ta gabata.
Matashin, Abdullahi Alhaji Bura ya ce dan majalisar ya ba shi aiki a hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA kuma yana aiki a reshen hukumar a Borno.
Abdullahi ya ce shi ma shaida ne kan wadanda aka ba aiki a jiya Litinin inda ya ce irinsu ba za su kirgu ba.
"Sunana Abdullahi Alhaji Bukar, ina daya daga cikin wandada ya ba aiki a NDLEA karshen 2023.
"Yanzu haka ina aiki a reshen hukumar da ke jihar Borno, ina da masaniyar wadanda aka ba aiki a jiya kuma yan mazabar ce, a gaba na aka ba su."
- Cewar Abdullahi Bukar
'Dan majalisa ya ba Borno tallafin N100m
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Borno ta kuma samun tallafi daga jagorori da yan siyasa a fadin Nigeria bayan iftila'in da ya faru na ambaliya.
Mummunan ambaliyar ruwa da jihar ta fuskanta a ranar Talata 10 ga watan Satumbar 2024 ta yi sanadin rasuwar mutane da dama da asarar dukiyoyin al'umma.
Rahotanni sun ce, dan majalisa mai wakiltar Biu/Bayo/Shani/Kwaya/Kusar, Hon. Mukhtar Betara ya mika tallafin N100m ga gwamnatin jihar bayan iftila'in da ya faru a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng