Hazikan sojoji sun sha kan yan ta’addan Boko Haram a fadan sa’o’i 7 da suka yi a garin Borno

Hazikan sojoji sun sha kan yan ta’addan Boko Haram a fadan sa’o’i 7 da suka yi a garin Borno

Daruruwan al’umman Gubio a jihar Borno a ranar Lahadi sun yi tururuwar fitowa tare da yin wakokin yabo ga hazikan dakarun sojin Najeriya, wadanda suka tunkari yan ta’addan Boko Haram/ISWAP bayan sun yi kokarin kai hari kan al’umman yankin.

Sun bayyana ra’ayinsu ne a lokacin da gwamnan jihar Borno, Babagana Umara ya ziyarci al’umman don gane ma idonsa abubuwan dake wakana.

Yayin da al’umman ke bayyana kokarin rundunar, sun fada ma Umaru cewa sojojin sun fuskanci yan ta’addan inda suka yi musayar wuta har na tsawon sa’o’i bakwai kafin su yi nasaran akansu.

A lokacin da ya ziyaransa zuwa Gubio, gwamnan ya kasance tawagan da ya hada da mamba mai wakiltan Gubio, Kaga da Magumeri a majalisan Tarayya, Usman Zanna da wassu jami’an gwamnati, sun ziyarci hedikwatan 5 Brigade na rundunan soji.

A taron tare da rundunan akwai kwamandan ‘Operation Lafiya Dole’, Manjo Janar Benson Akinroluyo;Kanal I.A Ajose, kwamandan Birgediya; Shugaba Mai rikon kwarya a Gubio, Zannah Modu Gubio, da sauran jami’an gwamnati.

Shugaba mai rikon kwaryan ya fada ma gwamnan cewa in ba don sojoji masu gwazon ba, da yan ta’addan sun samu shiga Gubio washegarin Sallah.

Yayin da yake nayar da martani, Gwamna Umaru ya yabi rundunar 5 Brigade akan kwazo da kuma kishin kasa da sojojin suka nuna a karkashin reshen.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan jihar Borno ya bayar da dajin Sambisa domin kafa Ruga

Gwamnan wanda ya ziyarci fadar hakimin, ya basu tabbacin cigaba da kasancewa da rundunar yan sanda.

Yayi amfani da taron wajen gabatar da motocin aiki ga yan bangan farar hula domin taimaka musu wajen kula da kauyuka, tattara bayanan kwararru, da kuma gudanar da aiki tare da rundunar soji.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel