Gwamnatin Kebbi za Ta Tura Dalibai zuwa Saudiyya, Ta Fadi Wadanda za Su Amfana
- Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya tura ɗalibai zuwa ƙasar Saudiyya domin yin karatu a fannin ilmin zamani da na addini
- Mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin addini, Imran bn Usman, ya bayyana cewa za tura ɗalibai 70 zuwa Saudiyya
- Injiniya Imran ya kuma bayyana cewa akwai shirin tura limamin masallatan Juma'a zuwa ƙasashen waje domin samun horaswa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta kammala shirye-shiryen tura ɗalibai zuwa ƙasar Saudiyya.
Gwamnatin jihar Kebbi ta shirya ɗaukar nauyin ɗalibai 70 zuwa ƙasar Saudiyya domin karatun digiri a ɓangaren ilmin zamani da na addini.

Asali: Facebook
Jaridar Tribune ta ce wannan shirin yana ƙarƙashin ofishin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin addini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kebbi za ta kai ɗalibai Saudiyya

Kara karanta wannan
Yadda jam'ian NDLEA suka cafke hodar iblis da za a kai Saudiyya cikin littattafan addini
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a ranar Litinin, mai bai wa gwamnan shawara ta musamman, Injiniya Imran bn Usman, ya bayyana cewa za a ɗauko ɗaliban ne daga ƙananan hukumomi 20 na jihar.
Ya ce kowace ƙaramar hukuma guda 20 da ke jihar za ta gabatar da sunayen ɗalibai uku, yayin da aka ware gurabe 10 ga Birnin Kebbi, babban birnin jihar.
"Gwamnatin jihar Kebbi za ta ɗauki nauyin tafiyar ɗaliban zuwa Saudiyya, yayin da gwamnatin Saudiyya za ta ɗauki nauyin karatunsu da kula da jin daɗinsu bayan sun isa."
- Injiniya Imran bn Usman
Injiniya Imran ya kara da cewa sai waɗanda shekarunsu ba su kai 18 ba za a ɗauka, kuma dole ne su tsallake matakin tantancewa domin cika sharuɗɗan da hukumomin Saudiyya suka gindaya.
“Masu tantance ɗalibai daga Saudiyya sun iso jihar Kebbi domin gudanar da gwajin da ake buƙata kafin tafiyar ɗaliban."
- Injiniya Imran bn Usman
An buƙaci kowace ƙaramar hukuma ta gabatar da ɗalibai maza biyu da mace ɗaya domin neman guraben karatun digiri na farko a fannin addini ko kuma wasu fannoni na ilmin zamani.

Asali: Twitter
Za a tura limamai zuwa ƙasashen waje
Baya ga wannan, mai bai wa gwamnan shawara ya sanar da wani shiri na tura limaman masallatan Jumu’a zuwa ƙasashen waje domin horaswa na ɗan ƙanƙanin lokaci a fannin gabatar da huɗuba da karatun Hadisi.
Ana kuma sa ran cewa ƙwararru daga birnin Riyadh za su ziyarci jihar Kebbi domin gudanar da aikin kula da mutane 5,000 da ke fama da matsalolin ido, inda za su sami magani kyauta, da haɗaɗɗun gilasan ido.
Har ila yau, ofishin jakadancin Saudiyya ya ba da kyautar Alkur’ani mai girma guda 10,000 ga jihar Kebbi.
Shirin Abin a yaba ne
Wani ɗan jihar Kebbi mai suna Lukman Isa Kamba ya yaba da matakin da gwamnati ta ɗauka na kai ɗaliban zuwa Saudiyya domin su yi karatu.
"Gaskiya wannan shirin abin a yaba ne, muna yabawa gwamnati kan wannan tsarin da ta fito da shi domin zai amfani al'umma."
"Muna yi wa waɗanda za su ci gajiyar shirin fatan alkhairi, Allah ya sa albarka a kan karatun su yi."
- Lukman Isa Kamba
Gwamnatin Kebbi za ta ɗauki ma'aikata
A wani labariin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta shirya ɗaukar sababbin ma'aikatan da za su koyar a makarantu.
Gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris za ta ɗauki sababbin malaman makaranta 2,000 domin inganta harkar ilmi a matakin firamare da sakandare.
Masu ruwa da tsaki a jihar sun yaba da matakin ɗaukar malaman, inda suka ce hakan zai bunƙasa ilmi a jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng