"Kai ne Ka Jawo": Atiku Ya Fadi Alakar Tinubu da Kisan Gillar Mutane 54 a Filato
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nuna damuwa tare da Allah-wadai kan kisan gillar da aka yi wa mutane 54 a Filato
- Atiku ya yi ikirarin cewa gazawar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan kare rayuka da dukiyoyin 'yan kasa ta jawo mutuwar mutanen
- Jigon na jam'iyyar PDP ya buƙaci a kafa kotuna na musamman don yanke shari’un ta’addanci, tare da ba jihohi ikon mallakar makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a 2023, Alhaji Atiku Abubakar, ya magantu kan kisan mutane a Filato.
Atiku ya zargi Shugaba Bola Tinubu da gazawa wajen hana kai hare-hare a Filato, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta da ƙwarewar da za ta kare rayuka da dukiyoyin 'yan ƙasa.

Asali: Facebook
'Bola Tinubu ya gaza kare rayuka' - Atiku
Atiku ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata, inda ya nuna alhini kan kisan akalla mutane 54 a garin Zike, ƙaramar hukumar Bassa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce wannan hari ya faru ne kwana kaɗan bayan makamancin sa a ƙaramar hukumar Bokkos, lamarin da ya kira "tabbatacciyar shaidar tabarbarewar tsaro" a ƙasar nan.
“Yadda ‘yan Najeriya ke rasa rayukansu saboda gazawar gwamnatin Tinubu abin takaici ne, kuma ba za mu ci gaba da lamunta ba,” inji Atiku.
Ya ce kare rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati, amma gwamnatin Tinubu ta gaza yin hakan.
Atiku ya kuma yi magana kan matsalar ta’addanci da ke ƙara ta’azzara a jihar Borno, yana danganta hakan da gazawar dabarun tsaron gwamnati.
Atiku ya nemi a ba jihohi damar mallakar makamai

Kara karanta wannan
'Ciwon ido': Jigon PDP ya faɗi mutane 2 da za su zama barazana ga ƴan adawa a 2027
Atiku ya ce gwamnatin tarayya ta kasa hukunta ‘yan ta’adda da masu aikata laifuffuka, inda wasu daga cikinsu aka kama su tun 2016 amma har yanzu ba a gurfanar da su a kotu ba.

Asali: Getty Images
“Idan da gwamnati na nuna irin ƙwazo wajen hukunta ‘yan ta’adda kamar yadda take nunawa wajen shari’ar masu adawa da ita, da tuni an tura sako mai ƙarfi ga ‘yan ta’adda,” inji Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci ministan shari’a da ya fi ba da fifiko ga shari’un ta’addanci, tare da buƙatar kafa kotuna na musamman don gaggauta yanke ire-iren wadannan shari’o'i.
Atiku ya kuma roƙi majalisar dokoki ta ƙasa da ta zartas da dokar da za ta bai wa gwamnatocin jihohi damar mallakar makamai da kayan aiki na zamani don ƙarfafa jami’an tsaro na cikin gida.
'Mutane 54 aka kashe a Filato' - Amnesty
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya nuna alhini kan mummunan harin da ya hallaka sama da mutane 50 a Filato, in da ya nemi a dawo da zaman lafiya.
Tinubu ya roki Gwamna Caleb Mutfwang da ya dauki matakin gaggawa wajen shawo kan rikicin, yana mai jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya mai dorewa.
Kungiyar Amnesty International ta ce mutane 54 aka kashe a harin, sannan ta bukaci gwamnatoci da su tashi tsaye wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng