Kisan Mutum 54: Bincike Ya Jefo Shakku a Adadin Wadanda aka Hallaka a Filato

Kisan Mutum 54: Bincike Ya Jefo Shakku a Adadin Wadanda aka Hallaka a Filato

  • Binciken hadin gwiwa ya gano kuskure a cikin adadin mutanen da aka ruwaito cewa an hallaka a jihar Filato a harin baya-bayan nan
  • Yayin da ake shirin birne mamata 17, jama'a sun firgita ganin yawan gawarwakin, wanda ya sa aka samu sabani a adadin wadanda aka kashe
  • An samu rahotanni daban-daban da ke cewa 'yan ta'adda sun hallaka mutane 51, yayin da wasu ke cewa an kashe mutum 34 zuwa 40

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Sababbin bayanai sun bayyana a kan yawan mutanen da 'yan ta'adda suka hallaka a harin baya-bayan nan da aka kai jihar Filato.

A baya, rahotanni daga yankunan da abin ya shafa sun bayyana adadi daban-daban na waɗanda suka mutu, wasu suka ce 51 ne, wasu suka ce 34, 40 ko 25.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

Filato
An gano kuskure a adadin mutanen da aka kashe a Filato Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Binciken da Zagazola Makama da hadin guiwar jami’an tsaro masu kula da zaman lafiya a jihar ya wallafa a shafin X cewa an gano gawarwaki 17 bayan sojoji sun yi aikin tsabtace yankunan da aka kai harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, majiya daga yankin da suka haɗa da cibiyar nazarin rikici ta Zagazola Media Network, wadda ta kai ziyara a ƙauyukan uku da aka kai harin, ta tabbatar da cewa mutum 17 aka birne.

Mutanen Filato sun firgita da hare-hare

Yayin da al’umma ke shirin gudanar da jana’izar mutanen, firgici ya mamaye su saboda fargabar cewa maharan na iya dawowa don kai sabon hari.

Dakarun Operation Safe Haven sun ƙara matsa kaimi, suka tura ƙarin jami’ai zuwa yankin da lamarin ya faru tare da gudanar da aikin bincike da kakkabe barazana.

Caleb
Gwamnan Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Asali: Twitter

Duk da wannan firgici, rahotanni daga yankin sun tabbatar cewa an kammala jana’izar, kuma mutum 17 ne kacal aka binne.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwato manyan bindigogi, sun gwabza fada da 'yan fashi

Kwamishinan ’yan sanda na Filato tare da Kwamandan Runduna ta 3, Birgediya Janar M.K. Sanda, sun kai ziyara ƙauyen Kwall don jajanta wa iyalan mamatan da kama maharan.

Jami’an tsaro sun ba jihar Filato kariya

Bayan harin, rahotanni sun nuna cewa dakarun tsaro sun kaddamar da sintiri a wurare da dama da suka haɗa da Gero, Te’Agbe, Rogochongo, Kpachidu, da Tafigana.

Sojoji da shugabannin al’umma sun tabbatar da jana’izar mutum 17, wannan ita ce sahihiyar sanarwar da ta fi dacewa game da wannan mummunan lamari.

A halin yanzu, babu ƙarin gawar da aka gano, sai dai jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin kama masu laifi da kuma hana sake faruwar irin wannan ta’asa.

Duk da ruɗani da rikice-rikicen alkaluma, sahihiyar adadin waɗanda aka kashe da aka birne ya tsaya ne a mutum 17.

Gwamnan Filato ya zauna da sojoji

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Filato ta tabbatar da wani mummunan hari da wasu 'yan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bassa da tsakar daren Lahadi, 14 ga Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutane sama da 100 da suka kai farmaki cikin dare a Abuja

Harin ya tayar da hankulan al’umma a faɗin ƙasar nan, inda ya haddasa asarar rayuka da kuma kona dukiyoyi, yayin da ake rika yada cewa an kashe mutane akalla 54 a harin.

Gwamna Caleb Muftwang ya yi zama na musamman da manyan jami’an tsaro da shugabannin kananan hukumomi don ƙarfafa matakan tsaro da hana maimaituwar irin wannan ta’asa a gaba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel