Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Wurin Ibada, Sun Yi Awon Gaba da Mutane

Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Wurin Ibada, Sun Yi Awon Gaba da Mutane

  • Ƴan bindiga sun kai hari kusa da wani tsauni a jihar Kogi, sun yi awon gaba da mutane suna tsakiyar ibadar dare
  • An ruwaito cewa maharan sun kutsa wurin ibadar ba za to ba tsammani, suka fara harbe-harbe kafin daga bisani su sace mutanen
  • Ƴan sa-kai sun yi kokarin daƙile harin amma maharan suka ci ƙarfinsu, suka tafi da masu ibadar da ba a tantance yawansu ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kogi - Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai farmaki wurin ibada a lokacin da mutane ke tsaka da bautar Ubangiji a wani tsauni da ke yankin Egbola, kusa da titin Agbaja, a karamar hukumar Lokoja ta jihar Kogi.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba daga cikin masu ibadar dare ta addinin kirista watau vigil.

Kara karanta wannan

Kisan mutum 54: Bincike ya jefo shakku a adadin wadanda aka hallaka a Filato

Kogi.
Yan bindiga sun sace masu ibada a jihar Kogi Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Lamarin ya faru ne a daren Juma’a lokacin da mabiya addinin ke gudanar da ibada a tsaunin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun farmaki wurin ibada

Shaidu sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga wurin ibadar su na harbi kan mai uwa da wabi domin tayar da hankula, kafin daga bisani su tilasta wa masu ibadar shiga daji tare da su.

Sai dai wata mata mai suna Mary Adams Gure ta samu kubuta daga hannun masu garkuwa da mutanen bayan sun kwashe su.

An ce matar ta kubuta ne da jami’an tsaron sa-kai na jihar, bayan sun samu labarin harin, suka garzaya wajen tare da fuskantar ‘yan bindigar, aka yi musayar wutan

Yadda ƴan sa-kai suka yi artabu da mahara

Wani daga cikin dakarun ƴan sa-kai ya bayyana cewa:

“Da muka samu labari, ba mu yi jinkiri ba, mu ka tashi cikin gaggawa mu ka tafi wurin domin kai ɗauki.

Kara karanta wannan

Ana shirin dakatar da samar da lantarki a Najeriya kan bashin Naira tiriliyan 4

"A wannan lokacin ne muka samu nasarar ceto Mary Gure. A yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran masu ibadar da aka sace.”

Gure ta samu damar tserewa a lokacin da aka fara musayar wuta, kuma daga bisani jami’an sa-kai suka taimaka mata ta samu mafaka, ta dawo gida cikin koshin lafiya.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Ba a samu jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ‘yan sanda na jihar Kogi, ASP William Aya, kan wannan sabon hari ba.

Kakakin ƴan sandan bai amsa kira ko sakonnin da aka tura masa ta wayar salula ba dangane da harin a lokacin da aka tuntube shi.

Sufetan yan sandan.
Yan sanda sun yi gum da bakinsu kan harin Hoto: @PoliceNG
Asali: Facebook

An sace ɗan sanda a birnin Abuja

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun yi garkuwa da wani jami'in rundunar ƴan sandan Najeriya a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

Ɗan sanda mai mukamin CSP, Modestus Ojiebe, wanda ke aiki a jihar Kwara, ya fada hannun ‘yan bindiga a kan babbar hanyar Kubwa da ke Abuja.

Bayan faruwar lamarin, rundunar 'yan sandan da ke yankin Dawaki ta samu kiran gaggawa, nan take ta tura tawagar sintiri zuwa wurin da abin ya faru.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel