Gwamnati Ta Fusata, Ta Sa An Dakatar da Shugaban Jami'ar FUOYE kan Zargin Lalata
- Gwamnatin tarayya ta dakatar da shugaban jami’ar FUOYE, Farfesa Abayomi Fasina, kan zargin lalata da wata Injiniya Folasade Adebayo
- Ministan ilimi ya fusata da rahoton kwamitin jami'ar da ya wanke Abayomi, inda ya nemi a dauki mataki, wanda ya haifar da taron gaggawa
- A yayin taron, kwamitin ya amince Farfesa Abayomi ya tafi hutun kwanaki 126, aka nada Farfesa Olubunmi Shittu a matsayin makaddashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ekiti - Gwamnatin tarayya ta sa an dakatar da shugaban jami’ar tarayya ta Oye-Ekiti (FUOYE) da ke jihar Ekiti, Farfesa Abayomi Sunday Fasina.
An dakatar da shugaban jami'ar ne bayan da wata babbar jami’ar makarantar, Injiniya Folasade Adebayo, ta zarge shi da yunkurin yin lalata da ita.

Asali: UGC
Minista ya tsoma baki a rigimar jami'ar FUOYE
Rahoton Sahara Reporters ya nuna cewa an dakatar da Farfesa Abayomi bayan da ministan ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya yi watsi da rahoton kwamitin gudanarwar jami'ar.

Kara karanta wannan
Portable: Ƴan sanda sun kama fitaccen mawakin Najeriya, an ji laifin da ya aikata
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce ministan ilimin ya nuna rashin rashin jin daɗinsa game da rahoton kwamitin hukumar gudanarwar jami’ar wanda ya wanke Farfesa Abayomi daga zargin.
Rahoton ya bayyana cewa kwamitin ya bukaci Injiniya Folasade ta nemi afuwar shugaban jami’ar, yayin da ya kuma yi watsi da korafin cin zarafin da ta shigar.
Wata majiyar jami’ar ta ce:
“Minista ya fusata da hukuncin kwamitin, yana ganin an yi ƙoƙarin yin rufa-rufa kan wannan zargi na cin zarafi, maimakon a yi sahihin bincike.
“Ya kira shugaban hukumar gudanarwar jami’ar, Sanata Victor Ndoma-Egba (SAN), inda ya bayyana masa rashin jin daɗinsa kan lamarin.”
An 'dakatar' da shugaban jami'ar FUOYE
Daga nan ne aka ce Sanata Victor Ndoma-Egba ya kira taron gaggawa na kwamitin hukumar a kafar intanet da karfe 2:00 na ranar Litinin, 14 ga Afrilu, 2025.
A yayin taron, kwamitin ya yanke shawarar tsige Farfesa Abayomi daga mukaminsa, sai dai cikin salo na tura shi hutun ritaya, maimakon kiran hakan da dakatarwa kai-tsaye.
Wasu majiyoyi sun ce Farfesa Abayomi ya roƙi kwamitin da ya ba shi damar tafiya hutun shekara da na nazari da ya nema, maimakon fuskantar dakatarwa.
Wata majiya ta shaida cewa:
“Ka san cewa idan shugaban jami’a yana shirin kammala wa’adinsa, musamman idan saura kasa da watanni shida, ana iya barinsa ya tafi hutu.
“Kodayake wa’adin Farfesa Fasina zai kare a watan Agusta, yanzu kwamitin ya umurce shi da ya tafi wannan hutu daga yau, Litinin 14 ga Afrilu, 2025.”
An nada shugabannin riko na jami'ar FUOYE

Asali: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa, a wata sanarwa da sakataren hukumar gudanarwa kuma magatakardar jami’ar, Mufutau A. Ibrahim, ya fitar, an ji cewa:
“Kwamitin gudanarwar jami’ar tarayya ta Oye-Ekiti (FUOYE) a taronta na gaggawa karo na 7 da aka gudanar ta kafar yanar gizo a ranar Litinin, 14 ga Afrilu, 2025, ya amince da bukatar Farfesa Abayomi Sunday Fasina na tafiya hutun shekara da na nazari, har na tsawon watanni shida (kwanaki 126 na aiki) daga cikin kwanaki 228 da ya rage masa, daga yau, Litinin 14 ga Afrilu, 2025.”

Kara karanta wannan
Abin da aka fadi ga Tinubu, Matawalle bayan aika riƙakken ɗan ta'adda lahira a Zamfara
A halin yanzu, kwamitin ya nada Farfesa Samuel Olubunmi Shittu, farfesa a fannin kimiyyar kasa, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban jami’a (bangaren karatu), a matsayin mukaddashin shugaban jami’ar na tsawon watanni shida.
Zargin lalata: An kori malamai a jami'ar Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin gudanarwar jami’ar tarayya ta Lokoja ya kori malamai hudu bisa laifin lalata da dalibai, domin kare mutuncin harkar ilimi a jami’ar.
Shugaban zaman kwamitin, Sanata Victor Ndoma-Egba, ya jinjina wa shugabancin jami’ar kan bin matakan doka da adalci yayin gudanar da binciken lamarin.
Kwamitin ya kuma bukaci jami’ar da ta gaggauta kammala sauran shari’o’in da suka shafi cin zarafin dalibai, musamman a sashen kimiyya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng