Sanatan APC Ya Bugi Kirji, Ya Fadi Sabuwar Jiha da Gwamnatin Tinubu Za Ta Kirkiro

Sanatan APC Ya Bugi Kirji, Ya Fadi Sabuwar Jiha da Gwamnatin Tinubu Za Ta Kirkiro

  • Ned Nwoko ya ce gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu na da shirin ƙirƙirar sabuwar Jihar Anioma a yankin Kudancin Najeriya
  • Sanata Nwoko ya bayyana hakan ne a yayin da shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya karbi daruruwan mutane zuwa jam'iyyar a Delta
  • A wajen taron, Ganduje ya tabbatar cewa ƙirƙirar Jihar Anioma batu ne da aka amince da shi, kuma APC da Tinubu sun yarda da kudurin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Delta - Sanata Ned Nwoko, ya bayyana kwarin guiwar cewa gwamnatin tarayya da APC a ƙarƙashin shugaba Bola Ahmed Tinubu za su ƙirƙiri sabuwar 'Jihar Anioma'.

Sanatan mai wakiltar Delta ta Arewa ya bayyana hakan ne a karshen mako a Delta, yayin wata ziyara da shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kai jihar.

Kara karanta wannan

APC ta tabo batun ajiye Kashim Shettima, ta ba Shugaba Tinubu shawara

Sanata Nwoko ya yi magana kan yiwuwar Tinubu ya amince da kirkirar jihar Anioma
Shugaba Bola Tinubu tare da Sanata Ned Nwoko a cikin fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @Prince_NedNwoko
Asali: Facebook

Tasirin ziyarar Ganduje a jihar Delta

Ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta kuduri aniyar magance gibin da ake da shi a tsarin rabon jihohi na yankuna ta hanyar kafa Jihar Anioma, inji rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sanatan, Michael Ogar ya fitar a Lafia, an ruwaito Sanata Nwoko yana cewa ziyarar Ganduje mataki ne mai muhimmanci wajen cimma adalci da daidaito a Najeriya.

“Wannan ziyarar alama ce da ke alamta cewa akwai kyakkyawan yakinin na kafuwar Jihar Anioma kuma wannan kuduri ya samu gindin zama a tsakanin mahukuntan ƙasa.
“Mutanenmu na da ‘yancin samun wakilci, kuma wannan shi ne hanya mafi dacewa don samar da adalci da daidaito a cikin tsarin shiyya na ƙasar nan."

- Inji sanarwar Michael Ogar.

APC ta samu sababbin 'yan jam'iyya a Delta

Ganduje ya ziyarci jihar ne domin halartar taron karɓar 'yan ƙungiyar Delta Unity daga mazabar tarayya ta Ika zuwa cikin jam’iyyar APC, wanda ya samu halartar manyan jiga-jigan APC daga jihohin Delta da Edo.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya yi fallasa, ya tono shirin Sanata Ndume kan jam'iyyar APC

Daga cikin su har da Sanata Ned Munir Nwoko, mai wakiltar shiyyar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, wanda ya taka rawa sosai a wajen taron.

A wajen taron, an ce Sanata Nwoko ya bayyana shigar kungiyar Delta Unity zuwa APC a matsayin “babban ci gaba ga siyasar Delta da al’ummar Anioma.”

"An kammala batun kirkirar jihar Anioma" - Ganduje

Ganduje ya yi magana kan kirkirar jihar Anioma
Shugaban kasa, Bola Tinubu tare da shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Yayin da yake jawabi ga magoya bayan APC, jiga-jigai da ƙungiyoyi daban-daban, Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Ganduje, ya ce an riga an tabbatar da kudurin ƙirƙirar Jihar Anioma.

Radio Nigeria (FRCN) ya rahoto cewa, Ganduje ya bayyana wa mahalarta taron cewa, “ƙirƙirar Jihar Anioma al’amari ne da aka rika aka kammala shi."

Ganduje ya tabbatar da cewa jam’iyya mai mulki, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnonin APC, majalisar tarayya suna goyon bayan wannan yunkuri na kirkirar sabuwar jihar.

Sanata Kalu ya goyi bayan kirkirar jihar Anioma

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya yi fallasa, ya fadi korafin jiga jigan APC kan Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Orji Uzor Kalu ya nuna cikakken goyon bayansa ga batun ƙirƙirar Jihar Anioma, wadda za ta zama jiha ta shida a yankin Kudu maso Gabas.

A cewar Sanata Kalu, kirkiro Jihar za ta taimaka wajen kawar da ra'ayin da wasu 'yan kabilar Igbo ke da shi na cewa ana nuna musu wariya a ƙasar nan.

Tun da farko, Sanata Ned Nwoko daga jihar Delta ya bayyana irin wannan goyon baya, yana mai cewa Jihar Anioma za ta gyara kuskuren tarihi da aka tafka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel