Bayan Hukunci Kotun ECOWAS, An Taso Gwamnatin Kano kan Batun Zagin Manzon Allah
- An sake taso gwamnatin jihar Kano kan dokar ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW biyo bayan hukuncin kotun ECOWAS
- Wata kungiyar kare haƙƙin ɗan adam (RID) ta buƙaci gwamnatin jihar Kano ta soke dokar domin guje wa tashin hankali
- Ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayyya ta tabbatar an aiwatar da hukuncin kotun ECOWAS wacce ta ce dokar ba ta dace ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Wata kungiyar kare hakkin dan adam a Najeriya mai suna Rivers in the Desert (RID) ta bukaci gwamnatin jihar Kano da ta soke dokokin batanci ga Annabi (S.A.W)
Kungiyar ta buƙaci a canza dokar wacce ke kunshi da hukuncin wanda ya taba mutuncin Manzon Allah SAW biyo bayan hukuncin da kotun ECOWAS ta yanke a ranar 9 ga Afrilu, 2025.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta tattaro cewa kotun ECOWAS ta bayyana dokar a matsayin wanda ba ta dace da kundin tsarin mulkin kasa da kuma hakkokin dan adam ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dokar ɓatanci: Kungiyar RID ta tsoma baki
A wata sanarwa da daraktan kungiyar RID, Adekunle James, ya fitar a ranar Litinin, ya ce:
“Ba zai yuwu ba a kasa mai bin tafarkin dimokuradiyya da ke girmama bambancin addini da ra’ayi ba, ace an tilasta dokar addini da ke take ‘yancin dan adam.”
RID Nigeria ta soki sashe na 210 da 382(b) na kundin laifuffuka na jihar Kano da dokar Shari’a, tana mai cewa dokokin sun yi nauyi fiye da kima.
Me dokokin ɓatancin Kano suka kunsa?
Dokar da ake ta ce-ce-ku-ce a kanta ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin zagi ko ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW a faɗin jihar Kano.
Dokar batanci a jihar Kano ta jawo hankalin duniya tun a shekarar 2020 lokacin da kotu ta yanke wa matashin mawaki Yahaya Sharif-Aminu hukuncin kisa kan wata waka da ya yi ta ɓatanci.

Kara karanta wannan
Muhyi ya kare kansa bayan zargin tozarta ma'aikatan gwamnatin Kano saboda ƴar tikok
Haka kuma, an yanke wa wani yaro, Omar Farouq, mai shekaru 13 a lokacin, hukuncin dauri na shekaru 10 kan zargin batanci, lamarin da ya jawo suka daga kungiyoyi da dama a duniya.
Ƙungiyar RID ta ce:
“Wadannan labarai ba tarihi ba ne kawai, su ne ainihin halin da ake ciki a Najeriya a karni na 21.”

Asali: Facebook
RID ta aika saƙo ga Gwamnatin Tarayya
Kungiyar ta yi kira da a girmama bambancin addini da ra’ayi da ke cikin Najeriya, tare da bayyana cewa matsayarta ba tana nuna adawa da addinin Musulunci ba ne.
RID ta gargadi gwamnatin Kano da kada ta ci gaba da amfani da dokokin da za su iya jefa rayukan mutane cikin hadari ko haifar da tashin hankali.
Ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta tabbatar an bi hukuncin kotun ƙungiyar kasashen yammacin Afirka watau ECOWAS.
Sanusi Isiyaku, wani bakano ya nuna damuwarsa kan yadda ƙungiyoyi ke neman yi wa jihar Kano katsalandan kan dokokinta.
Malamin makarantar ya shaida wa wakilin Legit cewa al'ummar Kano mafi yawa musulmi ne kuma sun amince da waɗannan dokoki.
Sanusi ya ce:
"Ni abin mamaki yake ba ni, kundin tsarin mulki ya ba jihohi damar su yi dokokin da suka dace da jama'arsu, shi yasa aka samar da Majalisar Dokoki a kowace jiha.
"Kano jihar musulunci ce, mune mafi yawa kuma mun yarda da waɗannan dokokin, me zai sa wasu daga can waje su sa mana baki? Na ji daɗin martanin gwamnatinmu mai albarka."
Gwamnatin Kano ta maida martani
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Kano karƙashin Abba Kabir Yusuf ta ce ba za ta soke dokokin ɓatanci ba duk da hukuncin ECOWAS.
Kotun ECOWAS ta yanke hukunci cewa wasu sashe na dokokin saɓo musamnan taɓa mutuncin Annabi na Kano ba su yi daidai da ka’idar kare hakkin dan Adam ba.
Sai dai gwamnatin Kano ta mayar da martani da cewa ba za ta canza dokokin ba saboda suna kare haƙƙin addinin musulunci ne.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng