Kotu Ta Bukaci FBI ta Kwancewa Tinubu Zani a Kasuwa kan Zargin Safarar Ƙwayoyi
- Wata kotu a Amurka ta umurci hukumar FBI da DEA su saki bayanan binciken da suka shafi Bola Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi
- Kotun ta ce bayanan da mai bincike Aaron Greenspan ya nema ta FOIA sun shafi Tinubu da wasu mutane uku da ke da alaƙa da zargin
- Hukumar FBI da DEA sun ce ba za su tabbatar ko musanta wanzuwar bayanan ba, amma kotu ta ce hakan ba daidai ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Columbia, USA - Wata kotun tarayya da ke Columbia a Amurka ta umurci fitar da bayanan bincike kan Shugaba Bola Tinubu.
Kotu ta umarci FBI da DEA su saki bayanan binciken laifuka da suka shafi Bola Tinubu kan zargin safarar miyagun kwayoyi.

Asali: Twitter
Buƙatar kotun Amurka game da zarge-zarge kan Tinubu
Alkalin kotun, Beryl Howell shi ya bayar da wannan hukunci a ranar 8 ga Afrilun 2025, cewar rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya umurci hukumomin su nemo su kuma sarrafa duk bayanan da ba su da kariya daga FOIA.
Aaron Greenspan, wanda ya kafa dandalin PlainSite, ya shigar da bukatun neman bayanai 12 daga 2022 zuwa 2023.
Bukatar Greenspan ta haɗa da bayanan Tinubu da wasu mutum uku: Lee Andrew Edwards, Mueez Abegboyega Akande da Abiodun Agbele.
FBI da DEA sun yi amfani da “Glomar response” wato ƙin tabbatarwa ko musanta wanzuwar bayanan, amma kotu ta ce hakan bai dace ba a wannan lamari.
An umurci FBI da DEA su gudanar da bincike kuma su saki duk wani bayani da ba ya ƙarƙashin kariya, sannan su kai rahoto zuwa kotu kafin 2 ga Mayu, 2025.
Hukuncin kotu ya ce:
“FBI da DEA sun tabbatar da cewa an gudanar da bincike kan Tinubu dangane da ƙungiyar safarar miyagun kwayoyi.
“Kowane hakkin sirri da ake tunanin yana tattare da bayanan FBI da DEA kan Tinubu, ya faɗi gaban bukatar jama’a ga sakin irin waɗannan bayanai.
“Tunda FBI da DEA ba su bayar da hujjar kare sirri kan cewa Tinubu yana ƙarƙashin binciken laifi ba, ba su iya kare amsar Glomar ba.”

Asali: Facebook
Abin da alkali ya ce kan lamarin
Kotu ta yarda da amsar CIA ta Glomar, bayan Greenspan ya amince cewa hukumar ta bayyana wanzuwar wasu bayanai masu alaƙa da bukatarsa, cewar Premium Times.
Alkali ya yanke hukunci cewa:
“Duk bayanin da aka tattauna a sama, mai shigar da ƙara ya cancanci samun hukuncin cin nasara kan amsoshin Glomar daga FBI da DEA.
“Saboda haka, FBI da DEA dole ne su gudanar da bincike kuma su sarrafa duk wani bayani da ba ya ƙarƙashin kariya da ya shafi FOIA.
Tinubu ya fara daƙile masu shirin komawa SDP
Kun ji cewa Bola Tinubu na kokarin hana manyan ‘yan siyasa daga bangaren CPC ficewa daga jam’iyyar APC zuwa SDP kafin zaben 2027.
An ce an shirya bai wa Sanata Tanko Al-Makura shugabancin jam’iyya don ya lallaso Buhari da magoya bayansa su ci gaba da kasancewa a APC.
Hakan ya zo bayan manyan jiga-jigan siyasa kamar Atiku, El-Rufai, Tambuwal na tattaunawa da Muhammadu Buhari kan barin APC.
Asali: Legit.ng