Abin Ya Fara Damun Tinubu, an 'Gano' Shirinsa kan Ƴan APC da Ke Son Komawa SDP

Abin Ya Fara Damun Tinubu, an 'Gano' Shirinsa kan Ƴan APC da Ke Son Komawa SDP

  • Shugaba Bola Tinubu na kokarin hana manyan ‘yan siyasa daga bangaren CPC ficewa daga jam’iyyar APC zuwa SDP kafin zaben 2027
  • Rahotanni sun ce an shirya bai wa Sanata Tanko Al-Makura shugabancin jam’iyya don ya lallaso Buhari da magoya bayansa su ci gaba da kasancewa a APC
  • Wasu manyan jiga-jigan siyasa kamar Atiku, El-Rufai, Tambuwal da Udenwa na tattaunawa da Buhari kan barin APC saboda rashin gamsuwa da shugabancin Tinubu
  • Yiwuwar ficewar CPC gaba daya na kara nuna raunin APC, yayin da jam’iyyar ke neman goyon bayan Buhari domin ceto martabarta kafin 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Yayin da shirye-shiryen zaben shugaban kasa na 2027 ke karfi, an gano shirin Bola Tinubu.

Rahotanni na nuna cewa Tinubu na kokarin hana ficewar jiga-jigan CPC daga APC zuwa jam'iyyar SDP.

Kara karanta wannan

Bayan ganawarsu, an tono bidiyo da Ganduje ke sukar Buhari kafin zaben Tinubu

Tinubu na shirin dakile masu son barin APC zuwa SDP
Wasu majiyoyi sun ce Tinubu na shirin dakile yan APC da ke son shiga SDP. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wata takardar sirri da ta bayyana ta nuna cewa Shugaba Tinubu na duba yiwuwar jan wasu jiga-jigai jikinsa da ba su mukami, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tururuwar yan adawa zuwa gidan Buhari

Wannan al’amari na faruwa ne a daidai lokacin da wasu jiga-jigan siyasa kamar Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Aminu Waziri Tambuwal ke duba sauya sheka daga APC.

Sun bayyana rashin jin dadinsu da salon mulkin Tinubu a matsayin dalilin da ya sa suke kokarin komawa wasu sabbin jam’iyyu kafin zaben shekarar 2027.

Abdullahi Ganduje da kungiyar gwamnoni na APC sun kara kokari wajen janyo Buhari don ya dakile yuwuwar ficewar mambobin tsohuwar jam'iyyar CPC.

A makon da ya gabata ne Gwamna Hope Uzodimma da wasu gwamnoni suka ziyarci Buhari a Kaduna domin rokon sa ya hana barin jam’iyyar APC.

Tinubu bai jin dadin shirin wasu yan APC da ke son komawa SDP
Majiyoyi sun ce Tinubu na shirin tayin mukamai ga wasu yan APC da ke shirin komawa SDP. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Wadanda ake zargin za su bar APC

Daga cikinsu akwai tsohon Gwamnan jihar Nasarawa a Arewa ta Tsakiya, Sanata Tanko Al-Makura.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa

Ana rade-radin cewa za a ba Al-Makura kujerar shugaban kasa na APC idan ya iya shawo kan Buhari da magoya bayansa su zauna a jam’iyyar.

Majiyoyi sun bayyana cewa Al-Makura zai yi taron manema labarai ranar Litinin, inda ake sa ran zai sanar da goyon bayan Buhari ga cigaba da kasancewa a APC.

An ce bangaren CPC na kunshe da mutane kamar Abubakar Malami da Emeka Nwajiuba, wadanda ke nuna rashin jin dadi da gwamnatin Tinubu.

Idan yan asalin tsohuwar jam'iyyarvCPC suka fice gaba daya, hakan na iya janyo mummunar illa ga damar APC a 2027 da haddasa ruɗani kan karfinta a siyasa.

2027: Tinubu ya sake samun goyon baya

Kun ji cewa wata ƙungiyar dattawa a yankin Kudu Maso Gabas ta nuna goyon bayanta ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Ƙungiyar ta ce yankin ya ci gajiyar mukamai ciki har da samun limamin babban masallacin Abuja na farko dan kabilar Ibo.

'Yan kungiyar sun roƙi Tinubu ya kawo kudurin ƙirƙirar sababbin jihohi tare da sauƙaƙa matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.