'Yan Sanda Sun Kwato Manyan Bindigogi, Sun Gwabza Fada da 'Yan Fashi

'Yan Sanda Sun Kwato Manyan Bindigogi, Sun Gwabza Fada da 'Yan Fashi

  • Rundunar ‘yan sanda ta ce ta ceto mutane 17 da aka sace a jihar Kaduna tare da hadin gwiwar ofishin Nuhu Ribadu
  • A wani samame na daban, jami'an rundunar sun kama wani mutum dauke da bindigogi 21 kirar AK-47 a cikin mota
  • A daya bangaren, jami'an ‘yan sanda sun yi artabu da ‘yan fashi a hanyar Kaduna-Abuja, suka kashe uku daga cikinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Rundunar ‘Yan Sanda ta Ƙasa ta samu gagarumar nasara a wasu manyan ayyukan tsaro da ta gudanar a jihar Kaduna a ranar 9 ga Afrilu, 2025.

Hakan ya biyo bayan umarnin da Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya bayar na kara kaimi wajen yaki da laifuffuka da kuma tabbatar da zaman lafiya a fadin ƙasa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutane sama da 100 da suka kai farmaki cikin dare a Abuja

Yan sanda
'Yan sanda sun ceto mutane 17 a Kaduna. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da ACP Olumuyiwa Adejobi ya wallafa X, ya bayyana cewa an samu nasarar ceto mutane 17 da aka sace daga Sarkin Pawa, jihar Neja, tun a ranar 3 ga Maris, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin ceto mutanen ya kasance ta hanyar hadin gwiwa da Ofishin Mai Baiwa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro (ONSA).

An ceto mata da aka sace a jihar Kaduna

Daga cikin wadanda aka ceto akwai yara ƙanana da mata da suka hada da Williams Ubadia, Samuel Ezekiel, Sunday Ezekiel, Jessy Friday, Favour Ezekiel mai shekara daya da sauransu.

An garzaya da su zuwa asibitin ‘yan sanda da ke Kaduna domin duba lafiyarsu, kuma duk an tabbatar da cewa lafiyarsu kalau.

An kama bindigogi 21 kirar AK-47

Haka zalika, a ranar da lamarin ya faru, jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane sun tare wata motar haya a kasuwar motoci ta Kawo.

Kara karanta wannan

Alkali ya sha da kyar bayan yan ta'adda sun yi ram da shi a Katsina

Bayan bincike mai zurfi, jami'an 'yan sanda sun gano bindigogi 21 kirar AK-47 da aka boye a cikin motar.

An kama matukin motar mai suna Jamilu Suleiman, dan shekara 27 da ya fito daga Rafin Guza, Kaduna.

Ya amsa cewa wani dan kungiyar direbobi ne ya umurce shi da ya kai makaman ga wani da ba a san ko waye ba.

'Yan sanda
'Yan sanda sun gwabza fada d 'yan fashi a Neja. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

'Yan sanda sun yi artabu da 'yan fashi

A wani lamari na daban, jami’an ‘yan sanda sun samu kiran gaggawa daga wani mai kishin ƙasa game da harin ‘yan fashi a Doggi Farm da ke hanyar Kaduna-Abuja.

DPO na Tafa ya jagoranci jami’ai zuwa wurin, inda suka yi musayar wuta da wasu ‘yan fashi har su 30.

An kashe biyu daga cikinsu nan take, yayin da wasu suka gudu. An kama wasu biyu da suka ji rauni, daya daga cikinsu ya rasu daga bisani a asibiti.

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya kamata a sani game da ranar 'yan sanda ta farko a Najeriya

An kama mutane sama da 100 a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja ta sanar da nasarar cafke wasu mutane sama da 100.

Legit ta rahoto cewa an kama mutanen ne a wani samame da 'yan sanda suka kai a unguwanni da dama na Abuja.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana irin kayayyakin da ta samu a tattare da mutanen tare da cewa za ta cigaba da farautar masu laifi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng