Gwamnati Ta Kammala Tantance Jakadu 109 da za Su Wakilci Najeriya a Kasashen Waje
- Gwamnatin Tarayya ta kammala tantance sunayen jakadu 109 da za su wakilci Najeriya a ofisoshin diflomasiyyar kasar guda 109
- An rika sa ran cewa Mai girma Shugaba Bola Tinubu zai tura sunayen jakadu da aka tantance ga Majalisar Tarayya tun ranar Laraba
- A Satumba 2023, gwamnatin Tinubu ta tsige jakadu sama da 83, kuma an ruwaito cewa tsoron kudin da za a kashe ya hana aika wasu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin Tarayya ta kammala tantance wadanda aka mika sunayensu don zama jakadu a ofisoshin diflomasiyyar Najeriya guda 109 da ke fadin duniya.
Wannan na kunshi ofisoshin jakadanci 76, ofisoshin babban jakada 22 da kuma ofisoshin hulda da jama’a 11 da ke kasashe daban daban.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa majiyoyi da dama da ke da masaniya kan batun sun tabbatar mata da cewa an kammala binciken tsaro da tarihin kowanne daga cikin wadanda aka mika sunayensu.
Tinubu bai aika sunayen jakadu ga majalisa ba
Rahoton ya kara da cewa ko da yake Shugaba Bola Tinubu ne ake sa ran zai mika jerin sunayen da aka tantance ga Majalisar Tarayya a farkon makon da ya gabata, har yanzu bai yi hakan ba.
A ranar 2 ga Afrilu, Shugaba Tinubu ya bar Abuja zuwa birnin Paris na kasar Faransa domin ziyarar aiki ta makonni biyu.

Asali: Facebook
A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce:
“A lokacin ziyarar, Shugaban kasa zai yi nazari kan yadda mulkinsa ke tafiya , da kuma tantance manyan nasarori da aka cimma."
Ya kara da cewa Shugaban kasa zai yi amfani da wannan lokaci wajen duba yadda sauye-sauyen da ake aiwatarwa ke tafiya.
Gwamnatin Tinubu za ta sanar da sunayen jakadu
Jami’ai da dama daga fadar shugaban kasa sun tabbatar cewa yanzu da an kammala tantance sunayen, ba da dadewa ba za a bayyana su.
Wani daga cikin jami’an da ya nemi a boye sunansa ya ce:
“Sun kammala binciken DSS. A gaskiya muna sa ran za a saki sunayen tun jiya ko ma kafin haka.
"Amma har yanzu, kamar dai Shugaban kasa na bukatar karin lokaci. Muna dakon ganin sunayen a wannan makon. Amma tabbas, bincike ya kammala.”
Wata majiyar daban ya bayyana cewa:
“An tsara a fitar da sunayen tun kafin jiya (Laraba). Ba mu da tabbas daga inda aka samu tsaikon.”
Yadda gwamnatin Tinubu ta tsige jakadu
Tun daga watan Satumban shekarar 2023, Shugaba Tinubu ya tunbuke jakadu sama da 83 tare da ba su umarnin su dawo gida.
A watan Disamba da ta gabata, wasu sahihan majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa Shugaba Tinubu ya yi amfani da wani lokaci na hutunsa sake duba kan batun.
Sai dai a watan Janairu, majiyoyi sun shaida cewa Shugaban kasa ya canja ra'ayi ne saboda yawan kudin da za a kashe, wanda ya kai kusan $1bn domin farfado da ayyukan ofisoshin jakadancin kasar a waje.
Masani na gargaɗi Najeriya kan rashin jakadu
Isma'il Ahmad, fitaccen masanin diplomasiyya ne a Kano, ya kuma shaida wa Legit cewa Najeriya ta yi kuskuren rashin naɗa jakadu da wuri.
Ya ce akwai abubuwa da dama da kasar za ta rasa saboda rashin samar da wakilci a sauran ƙasashen duniya da ta ke da alaƙa da su.
Isma'il Ahmad ya ce:
""Ai tamkar ma ka nuna wa duniya cewa ana dama wa babu kai a ciki, ba ka da faɗa a ji, baka da ruwa da tsaki. Idan har ƙasa ba ta da jakada a wata ƙasar ko kuma a ƙasashe da dama, za ta rasa abubuwa da yawa."
Shehu ya samu shiga jerin jakadun Najeriya
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta fara tantance wasu 'yan siyasa a kokarinta na cike ofisoshin jakadanci 76 da manyan ofisoshin jakadu 22 da Najeriya ke da su a waje.
Wannan mataki na tantancewa ya biyo bayan bukatar tabbatar da sahihancin wadanda za a nada a manyan mukamai na diflomasiyya, bayan Najeriya ta dade ba ta da wakilci a kasashen waje.
A cikin jerin sunayen da aka fara tantancewa an ce akwai Sanata Shehu Sani, wanda kwanan nan ya koma jam’iyyar APC, da kuma tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng