Jihohin Arewa 6 Sun Koka kan Ware Su a Shirin Noman Tinubu na Dala Miliyan 530

Jihohin Arewa 6 Sun Koka kan Ware Su a Shirin Noman Tinubu na Dala Miliyan 530

  • ‘Yan majalisun Arewa maso Gabas sun nuna bacin rai bisa cire yankin daga tsarin bunkasa noma da masana’antu na gwamnatin tarayya
  • Shugabansu na yankin, Sanata Danjuma Goje, ya ce cire Arewa maso Gabas daga tsarin ya sabawa adalci da ci gaban da aka yi alkawari
  • Shirin ya ƙunshi $530m daga gwamnati da abokan hulɗarta, amma ba wata jiha daga Arewa maso Gabas da aka ambata a matakin farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - ‘Yan majalisun Arewa maso Gabas sun bayyana rashin jin daɗi bisa ware jihohin yankin daga tsarin musamman na bunkasa noma da masana’antu (SAPZ) na gwamnatin tarayya.

Korafin ya fito ne daga Sanatoci da ‘yan majalisun wakilai daga jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, inda suka gudanar da taron gaggawa a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kwato manyan bindigogi, sun gwabza fada da 'yan fashi

Arewa
'Yan majalisun Arewa maso gabas sun ce an ware su a shirin noman Tinubu. Hoto: Muhammad Adamu
Asali: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Sanata Danjuma Goje da ke wakiltar Gombe ta tsakiya ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuƙa duba da albarkatun noma da kiwo da yankin ke da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Korafin 'yan Arewa maso Gabas ga Tinubu

A cewar Goje, shirin SAPZ da aka ƙaddamar ranar Talata, 8 ga Afrilu, 2025 a jihar Kaduna, zai ƙunshi gudummawar dala miliyan 530 daga gwamnatin tarayya.

Haka zalika Bankin Raya Afirka (AfDB), Bankin Musulunci na IsDB, da Asusun Raya Noma na Duniya (IFAD) za su tallafawa shirin.

Sai dai Goje ya ce a jerin jihohin da aka zaɓa, babu ko guda daga Arewa maso Gabas, inda wasu jihohi kamar Kaduna, Kano, Ogun da Oyo suka samu kaso sama da daya.

Ya ce hakan ya nuna rashin daidaito da kuma kaucewa burin gwamnati na haɗa kan kowa da kowa cikin tsarin raya ƙasa da bunƙasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Akpabio ya fadi abin da ya sani kan yunkurin hallaka Sanata Natasha

Albarkatun noma a Arewa maso Gabas

Sanata Goje ya ce yankin Arewa maso Gabas yana da fadi a Najeriya, kuma yana da tasiri wajen samar da dabbobi da amfanin gona da ke karfafa tattalin Najeriya.

Premium Times ta rahoto Sanata Danjuma Goje ya ce:

“Mun damu ƙwarai da gaske da yadda aka ware mu a wannan. Hakan ya sabawa shirin raya noma da rage asarar amfanin gona bayan girbi.”

Me 'yan Arewa maso Gabas ke bukata?

Sanata Goje ya yi kira da a gaggauta sanya yankin Arewa maso Gabas cikin shirin SAPZ domin tabbatar da adalci da kuma aiwatar da manufar gwamnatin shugaban ƙasa na bunƙasa noma.

Ya ƙara da cewa sanya yankin zai taimaka wajen ƙirƙiro da cibiyoyin sarrafa amfanin gona, haɗa manoma da masana’antu, da kuma bunƙasa tattalin arzikin karkara a Najeriya.

Arewa
Arewa maso Gabas ta bukaci a sanya ta a cikin shirin noman gwamnatin Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Ndume ya zargi Tinubu da nuna wariya

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa a Edo: Majalisa na neman sauya fasalin aikin 'yan banga

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya yi korafin cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu na nuna wariya.

Sanata Ali Ndume ya ce Bola Tinubu ya ware wasu yankunan Najeriya wajen nada mukaman gwamnati.

Ali Ndume ya ce hakan ya saba da kundin tsarin mukin Najeriya da tsarin raba mukamai na kasa, inda ya bukaci a yi gyara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng