Sauki Ya Zo: Farashin Kayan Abinci Ya Sauka a Kasuwa, An Ji Kudin Shinkafa a Yobe
- An samu ragin farashin masara, dawa da gero a kasuwar hatsi ta Potiskum, amma farashin wake ya tashi, ya koma N90,000-N97,000
- Buhun dawa fara ya koma N36,000-N37,000, dawa 'yar Kaura ya koma N41,000-N43,000 yayin da dawa 'yar Wala ta sauka zuwa N35,000
- Rahoto ya ce ridi dan gauraye da barkono dan Gashua sun koma N60,000, yayin da shinkafa mai aure ta sauka zuwa N51,000 a kasuwar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Yobe - An samu saukar farashin kayan abinci a kasuwar hatsi ta karamar hukumar Potiskum da ke jihar Yobe.
Wannan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke murnar saukar farashin fetur a matatar man Dangote daga N888 zuwa N865.

Asali: Facebook
An ji farashin gero, dawa a kasuwar Potiskum
Wani rahoto na farashin kayan hatsin da wani Idriss Zakari Yobe ya tattaro, wanda @abbkar_ai ya wallafa a shafinsa na X, ya nuna cewa wake ya kara kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton farashin hatsi a kasuwar Potiskum na ranar Laraba, 9 ga watan Afrilu, 2025, an samu ragin kudin dawa, masara da gero.
Rahoton ya nuna cewa ana sayar da buhun gero a tsakanin N45,000 zuwa N47,000 yayin da buhun 'ya'yan taba ya sauka zuwa N16,000-N17,000.
Hakazalika, rahoton ya nuna cewa farashin buhun dawa 'yar Kaura ya koma N41,000-N43,000 yayin da dawa fara ta koma N36,000-N37,000.
Farashin wake ya haura zuwa N95,000 a Yobe
Ita ma dai dawar Kwakwai ta sauka, amma ba a bayyana kudin da ake sayar da ita yanzu ba, yayin da aka ce farashin farin wake babba ya koma N90,000-N95,000.
Kananun fararen wake kuwa ana sayar da buhunsu yanzu a kan N90,000-N92,000, inda shi kuma jan wake ake sayar da shi a kan N95,000 zuwa N97,000.
A kasuwar hatsi ta Potiskum, kamar yadda rahoton ya nuna, buhun dawa 'yar Wala (Wuyo) ya sauka zuwa N35,000-N36,000.
Shinkafa mai aure ta sauka zuwa N51,000

Asali: Twitter
Amma an ce farashin ridi da aka gauraya yana nan a kan N60,000 kan kowane buhu, yayin da hatsin gurguzu ake sayar da shi a kan N20,000.
Amma ba a iya sanin farashin buhun gurguzu na zobo ba, sai dai an ce farashin buhun shinkafa mai aure (iri na musamman) ya kai N51,000.
Farashin buhun Gujjiya ya kai har N160,000 yayin da ake sayar da buhun barkono dan garin Gashua a kan N60,000.
Duba farashin kayan a kasa:
Dangote ya sauke farashin man fetur
Tun da fari, mun ruwaito cewa matatar man Dangote ta sauke farashin litar man fetur da take sayar wa 'yan kasuwa daga N888 zuwa N865, ragin N15.
Yayin da matatar ta yi wa 'yan kasuwa wannan ragi, 'yan Najeriya na fatan cewa za a ga wannan sauyi a gidajen man 'yan kasuwar da ke fadin kasar.
Wannan ci gaban na zuwa ne yayin da gwamnatin tarayya ta sanar da ci gaba da sayar da danyen mai ga matatun Najeriya a kan Naira maimakon dala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng