Gwamnati Ta Zakulo Talakawa 6,000 a Nasarawa, za a Raba Masu Naira Miliyan 42

Gwamnati Ta Zakulo Talakawa 6,000 a Nasarawa, za a Raba Masu Naira Miliyan 42

  • Hukumar jin dadin jama’a ta Nasarawa ta ce talakawa da mabukata 6,000 za su ci gajiyar zango na biyu na tallafin kudi daga gwamnatin jihar
  • Shugaban hukumar, Imran Usman ya ce ana ba talakawa N7,000 a wata, kuma shirin zai gudana har watanni 24 a kananan hukumomi 13
  • Imran ya ce gwamnatin jihar a karkashin shirin ta na karfafa gwiwar masu sana’o’in hannu, inda ake ba masu kokari karin N50,000 ko N30,000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Nasarawa - Hukumar bunkasa jama’a ta jihar Nasarawa ta ce mutane 6,000 za su ci gajiyar zango na biyu na shirin bayar da tallafin kudi da gwamnatin jihar ta kirkiro.

Daraktan hukumar, Imran Usman, ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a karamar hukumar Keffi ta jihar.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun bude wuta da aka yi yunkurin kai hari gidan Kashim Shettima

Gwamnatin Nasarawa ta na rabawa mutane 6,000 tallafin N7000 duk wata
Gwamnatin Nasarawa na ci gaba da rabawa mutane 6,000 tallafin N7000 duk wata. Hoto: @NasarawaInvest
Asali: Twitter

Mutane 6,000 za su samu N7,000 a Nasarawa

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Imran ya yi magana ne a lokacin da aka fara raba kudaden tallafin ga wasu daga cikin masu cin gajiyar shirin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Imran, gwamnati ta na ba da tallafin N7,000 ga kowane mutum daga cikin talakawan da aka zakulo a kananan hukumomi 13 na jihar, a kowane wata.

“Wannan shi ne zangon 15 na shirin, kuma ana sa ran zai dore har tsawon watanni 24. Kamar yadda kuke gani, muna kokari sosai wajen aiwatar da wannan shiri.”
“Yanzu haka, ana bai wa masu cin gajiyar shirin N7,000 a kowane wata, sabanin N5,000 da ake bayarwa a lokacin da aka fara shirin."

- Inji Imran Usman.

Nasarawa: Hazikan masu sana'o'i na samun N50,000

Shugaban hukumar ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan bayar da wannan tallafi shi ne karfafa gwiwar talakawa su fara sana’o’in hannu domin su dogara da kansu.

Kara karanta wannan

Bayan Wike ya gana da 'yan majalisa, an bijirewa kotu, an yi nadin mukamai a Rivers

A cewar Imram Usman:

“Zan iya cewa muna da labarai da dama na nasarorin da muke samu a wannan fanni. Mun kafa wata hanya ta sa ido, inda muke zagaya wa domin ganin yadda masu cin gajiyar shirin ke tafiyar da sana’o’insu.
“Muna ba su karin karfin gwiwa da kuma wata gudunmawa ta N50,000 ko N30,000 bisa ga yawan kudin da muke da su a lokacin."

Daraktan ya bayyana cewa a zangon farko na shirin a lokacin mulkin farko na Gwamna Abdullahi Sule, adadin wadanda suka ci gajiyar shirin ya kai 3,800, kuma kowanne na karbar N5,000.

Yadda talakawa, zawarawa ke cin gajiyar shirin

Gwamnatin Nasarawa ta yi magana kan N7000 da take rawaba talakawa 6,000 duk wata
Gwamnatin Nasarawa ta bayyana wadanda take rabawa tallafin N7,000 duk wata. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Imram Usman ya yi bayani cewa:

“Yanzu haka muna da mutane 6,000 da ke cin gajiyar shirin kuma muna bai wa kowanne daga cikinsu N7,000. Zuwa yanzu, komai yana tafiya lafiya ba tare da wata tangarda ba.
“Ina godiya sosai ga gwamna saboda kasancewarsa shugaba mai kulawa da rikon amana, wanda ke cika alkawari kuma bai taba gazawa wajen taimaka wa mabukata ba.

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

“Ba abin mamaki ba ne ka ce 'N7,000 ba kudi masu yawa ba ne', amma ka sani cewa, ga wadannan mabukata, kudin na da matukar muhimmanci a gare su.
"Muna da tsofaffi da talakawa, muna da zawarawa da ke amfana da wannan tallafi, kuma suna kula da kansu da iyalansu daga wannan kudi."

Gwamna Abdullahi ya kare tallafin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Abdullahi Sule na Nasarawa ya bayyana cewa, N8,000 na iya zama kuɗi masu yawa ga wasu iyalai da ke fama da talauci.

Ya ce ko da yake wasu za su iya ganin kuɗin ba su da wani yawa, amma akwai magidanta da dama da ba su cika samun irin wannan adadi a cikin wata ɗaya ba.

Gwamnan ya kare shirin gwamnatin tarayyana raba N8,000 duk wata ga miliyoyin iyalai na tsawon watanni shida, domin rage radadin cire tallafin fetur.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel