Gwamnati za ta raba wa talakawa naira dubu biyar-biyar a watan Yuli
Gwamnatin Tarayya za ta fara bawa wa talakawa tallafin naira budu biyar daga watan Juli mai kamawa.
Za a fara ne da raba kudin a wasu jihohi 19 da aka ware. Jihohin dai sun hada da: Niger, Kogi, Ekiti, Osun, Oyo, Kwara, Cross River, Bauchi, Gombe, Jigawa, Benue, Taraba, Adamawa, Kano, Katsina, Kaduna, Plateau, Nasarawa, Anambra da kuma sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno.
Za a dunga bayar da tallafin kudin ne a kowane wata.
Jami’in Raba Kudaden Tallafin ta Hanyar Asusun Ajiyar Banki, Tukur Rumar ne ya sanar da wannan cigaban.
Ya ce kudaden da za a raba din duk za su fito ne daga cikin dala milyan 322 da aka dawowa Najeriya das hi na kudin da tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya boye a kasashen Turai.
Idan ba a manta ba, har bayan da Buhari ya karbi kudin da Abacha ya boye a kasashen waje, ya sha cewa Abacha bai wawuri dukiyar kasa ba, mutum ne mai gaskiya da rikon amana.
KU KARANTA KUMA: Sarki ya karrama yaron da ya haddace cikakken Al-Qur'ani a shekara 3
Sai dai kuma ba kowane mutum daya ne za a bai wa kudin ba, gida-gida ne za a rika bai wa.
Wato kowane gida za a bai wa mutane gidan naira dubu biyar. Gwamnati ta ce gidaje 302,000 ne za su amfana a cikin jihohin 19.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng