FG ta sanar da fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu 300,000 a jihohi 11

FG ta sanar da fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu 300,000 a jihohi 11

- Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin bawa masu sana'ar hannu tallafin N30,000

- An fara biyan tallafin ga masu sana'ar hannu 300,000 a rukunin farko na shirin bayar da tallafin

- An zabi mutanen da zasu ci moriyar shirin a wannan daga jihohi goma da ke sassa daban-daban na Najeriya

A yayin da batagarin mutane ke tsaka da cigaba da barna a sassan kasa, gwamnatin tarayya ta sanar da kaddamar da shirin bunkasa tattalin arziki.

A karkashin wannan shiri, gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu.

A cewar gwamnatin tarayya, za ta biya kudin sau daya ga kowanne mutum.

Kudin da aka fara rabawa na daga cikin kudaden da aka ware domin farfado da kananan masana'antu da bullar annobar korona ta kassara.

An fara biyan kudaden ne kai tsaye zuwa asusun masu sana'ar hannu da aka tantance a jihohi goma.

KARANTA: Nadin sarauta: Fusatattun matasa sun kutsa fadar babban Sarki, an kubutar da shi da kyar

Jihohi 10 da aka zaba a matsayin rukuni na farko tare da fara biyan mutanensu sun hada da; Abuja, Lagos, Kaduna, Ondo, Kano, Borno, Abia, Bauchi, Anambra, Ribas, Filato, da Delta.

Mutanen da aka zaba daga jihohin sun aika bayanansu ne a tsakanin 1 ga watan Oktoba zuwa ranar 10 ga watan Oktoba ta shafin yanar gizo da aka bude domin neman tallafin.

FG ta sanar da fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu 300,000 a jihohi 10
Masu kananan sana'o'i
Asali: Original

Shugaba Buhari ne ya kaddamar da shirin bawa kananan masana'antu tallafi (MSMEs Survival Fund) a cikin watan Maris, 2020.

Shirin ya na daga cikin babban tsarin raya tattalin arziki (NESP) wanda shugaba Buhari ya nada mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya zama jagora.

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar hutun bikin Mauludi

A saboda haka, ofishin Osinbajo ne zai sa ido a kan kaddamar da shirin tare da tafiyar da komai bisa manufofi da ka'idojin da gwamnati ta gindaya.

An tura masu yi wa jama'a rijista zuwa sauran jihohin da za a bayar da tallafin a sauran rukunai da zasu biyo baya nan gaba.

Gwamnati ta shawarci masu sana'o'in hannu su tuntubi shugabannin kungiyoyinsu domin mika sunayensu.

Tuni aka fara rijistar mutane a rukuni na biyu daga ranar 19 ga watan Oktoba a jihohin Edo, Ogun, Ekiti, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Enugu, Ebonyi, Adamawa, Taraba, da Bayelsa.

A bangare guda, har yanzu ana cigaba da tantance bayanai da takardun wadanda suka nemi tallafi 'tada komada' a karkashin tsarin tallafawa masu matsakaitan masana'antu da aiyukansu suka tsaya lokacin annobar korona.

Sai dai, ba a sanar da lokacin da za a fara biyan wannan rukuni na masu masana'antu ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng