"Tsaro Ya Inganta a Jihar Katsina," Nuhu Ribadu Ya Kai Ziyarar Ta'aziyya ga Gwamna

"Tsaro Ya Inganta a Jihar Katsina," Nuhu Ribadu Ya Kai Ziyarar Ta'aziyya ga Gwamna

  • Malam Nuhu Ribadu ya kai ziyarar ta'aziyya ga Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina bisa rasuwar mahaifiyarsa
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce alamu sun nuna cewa an samu raguwar matsalar tsaro a jihar Katsina
  • Ribadu ya ce Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da goyon bayan ƙoƙarin da Katsina take yi na dawo da tsaro da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya tabbatar da cewa an samu gagarumar ci gaba a fannin tsaro a Jihar Katsina.

Malam Ribadu ya ce abubuwan da ke faruwa a Katsina yanzu na nuna cewa ana samun nasara a yaki da matsalar tsaro da ake yi.

Malam Dikko Radda da NSA
Nuhu Ribadu ya ce an samu tsaro a Katsina Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Asali: Facebook

Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Gwamna Dikko Umaru Radda bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u Umaru Barebari, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta kawo tallafin N300bn, mutum 1 zai iya samun N10m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsaro ya inganta a jihar Katsina

Yayin da yake magana da manema labarai, Ribadu ya ce:

"Mu na ganin yadda sha'anin tsaro ya inganta a jihar Katsina. Kowa na iya tabbatar da cewa abubuwa na kara kyau. Da ikon Allah, za mu kai ga lokacin da mutane za su koma rayuwa cikin kwanciyar hankali da natsuwa.”

Ribadu ya bayyana cewa ko da yake samun cikakken zaman lafiya na ɗaukar lokaci, amma ya yaba da yadda Gwamna Radda ke jagorantar Katsina da haɗin gwiwar hukumomin tsaro wajen tunkarar sha'anin tsaro.

Ya kara da cewa:

"Ba za mu ce zaman lafiya ya dawo dari bisa dari ba, domin matsalar ta dauki lokaci kafin ta yadu, amma muna kan turba mai kyau, nasarorin da aka samu kawo yanzu abin a yaba ne.”

Gwamnatin Tinubu na goyon bayan Katsina

Ribadu ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na goyon bayan ƙoƙarin da gwamnatin Katsina ke yi na ganin matsalar tsaro ta zama tarihi.

Kara karanta wannan

Kano: Buba Galadima ya yi maganar yiwuwar sake sauke Sanusi II da maido shi

Ya yaba da tsarin da Katsina ta ɗauka na amfani da fasaha da tattara bayanan sirri wajen magance matsalar ta tsaro.

Wannan ziyara ta Nuhu Ribadu na zuwa ne bayan rasuwar mahaifiyar gwamnan, ya mika sakon ta’aziyya a madadin gwamnatin tarayya da kuma Majalisar Tsaron Ƙasa.

Gwamnatin Katsin ta godewa Nuhu Ribadu

A jawabinsa na godiya, Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe, ya yaba da ziyarar da kuma kalaman da hadimin ya yi.

“Wannan ziyara ta kara tabbatar da kudurinmu na aiki tare domin wanzar da zaman lafiya, tsaro da ci gaba,” in ji shi.

Ribadu ya samu rakiyar manyan jami’ai da suka hada da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Umar Buba, Janar Sarkin Yaki Bello (mai ritaya), da wasu manyan jami’ai na gwamnati.

Nuhu Ribadu ya nemi a daina biyan fansa

A wani labarin, kun ji cewa Malam Nuhu Ribaɗu ya gargaɗi ƴan Najeriya su daina biyan kuɗin fansa ga ƴan bindiga idan sun yi garkuwa da ƴan uwansu.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya fadi hanyar kawo karshen kisan gilla a jihar Filato

An ji ya ƙarfafawa mutane guiwa da cewa dakarun sojojin Najeriya suna iya bakin ƙoƙarinsu kuma sun ceto mutane da yawa daga hannun masu garkuwa.

A cewarsa, biyan kuɗin fansa ba komai yake jawo wa ba face ƙara wa ƴan ta'adda ƙarfi su ci gaba da aikata miyagun laifuffuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel