An Buga Asara a Kano da Mummunar Gobara ta Tashi a Kasuwar Gandun Albasa
- Masu sana’ar hada kayan daki a kasuwar Gandun Albasa, Kano, sun shiga damuwa bayan gobara ta kone shaguna cikin dare
- Ganau sun ce gobarar ta tashi ne bayan da aka dawo da lantarki da karfi da misalin karfe 10:00 na dare ranar Alhamis, 10 ga Afrilu 2025
- Mu'azu Indabawa ya bayyana cewa an yi asarar miliyoyin Naira, yayin da ya jinjinawa hukumar kashe gobara kan daukin gaggawa da ta kai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Masu sana’ar hada kayan daki a kasuwar Gandun Albasa, a jihar Kano sun shiga tashin hankali da wata mummunar gobara ta babbake shagunsu.
Wannan na zuwa ne 'yan awanni bayan da muka rahoto cewa gobara mai tsanani ta tashi a babbar kasuwar Zamfara, inda shaguna 55 suka kone.

Asali: UGC
Kano: Gobata ta tashi a kasuwar Gandun Albasa
A rahoton da jaridar Daily Trust ta fitar, an ce gobara ta tashi a kasuwar Gandun Albasa da ke kusa da filin baje kolin kasuwanci na Kano a daren ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wurin da gobarar ta tashi sananne ne wajen hada kayan daki a Kano, kuma yana samar da hanyoyin dogaro da kai ga daruruwan masu sana’a da ‘yan kasuwa.
Ganau sun bayyana cewa gobarar ta samo asali ne daga wutar lantarki da ta dawo da karfi da misalin karfe 10:00 na dare, wanda ya haddasa gobarar ta bazu cikin gaggawa.
Shaguna biyu da aka ce suna shake da katifu sun kone kurmus, yayin da wasu shaguna biyu da ke dauke da kayan daki da aka gama hada su suka cinye da wuta.
'Yan kasuwa sun kirga asara mai yawa a Kano

Asali: Original
Wani mai shago, Mu’azu Inuwa Indabawa ya kiyasta cewa an yi asarar da ta kai miliyoyin naira a wannan gobarar, lamarin da ya jefa 'yan kasuwa a damuwa sosai.
Mu'azu Inuwa ya kuma yabawa hukumar kashe gobara ta jihar Kano, kan daukin gaggawa da ta kawo, wanda ya hana wutar bazuwa zuwa sauran shagunan kasuwar.
“Ginin da ke dauke da shagunan Hausawa Best Furniture, Shamsu Sabiu Isa Furniture, Shuaibu Anamu Best Furniture, da kuma Indabawa Furniture ya kone gaba daya.
"Daya daga cikin shagunannin yana cike da katifu, kuma babu katifa ko daya da aka iya ciro wa da wutar ta kama"
- Inji Indabawa.
Duk da haka, an ce wani ginin bene da ke makwabtaka da wurin, wanda ke dauke da karin kayan daki, da wasu shaguna da ke makwabtaka da su, sun kubuta daga gobarar.
Rahoton gobarar da ta afku a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa gobara ta kashe mutane bakwai a cikin watan Fabrairun 2025.
Hukumar ta kuma ce ta ceto rayukan wasu mutane bakwai da kuma dukiyar da darajarta ta kai Naira milyan 180 a wurare daban daban da gobara ta tashi.
Kabiru Isa Jaafar, wanda ya yi magana madadin mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf, ya ce sun karbi kiran gaggawa na afkuwar gobara har sau 77.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng