Inna lillahi wa inna ilaihi Raji’un: Yadda wuta ta cinye kasuwar kifi dake garin Baga (Hotuna)
Wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar kifi dake garin Baga cikin garin Maiduguri na jihar Borno, wanda ta janyo mummunan asara ga yan kasuwa, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito gobarar ta fara ne da misalin karfe 10:30 na daren Lahadi, 12 ga watan Agusta, kamar yadda wani dan kasuwar, Muhammad Labo ya bayyana, Sa’annan ya bayyana kokarin da jami’an kwana kwana suka yi wajen hana gobarar shiga sauran sassan kasuwar.
KU KARANTA: Magidanci ya sheme yayarsa har lahira kan zarginta da cinye masa diya da maita
“Mun rufe shagunanmu mun tafi gida kenan sai aka kiramu wai kasuwarmu ta kama da wuta, da dama daga cikin shagunanmu sun kone kurmus, a yanzu haka muna ta kokarin kashe wutar, amma matsalar wutar lantarki ce ta janyo gobarar.” Inji shi.
Kaakakin hukumar kashe wuta ta jihar Borno, Ambursa Pindar ya tabbatar da faruwa lamarin, inda yace hukumar ta yi maza maza wajen aikawa da motocin kashe wuta guda hudu zuwa kasuwar don haka ya bada tabbacin zasu kashe wutar.
Daga karshe Kaakakin yace zasu gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar gobarar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng