Kisan Hausawa a Edo: Majalisa na Neman Sauya Fasalin Aikin 'Yan Banga
- Kwamitin Sojin ƙasa na Majalisar Wakilai ya yi kira da a bayar da horo da kuma sanya ido kan ƙungiyoyin 'yan banga a Najeriya
- Babban dalilin wannan kira ya biyo bayan kisan wasu 'yan Arewa 16 da aka yi a Uromi, jihar Edo, wanda ya tada kura a faɗin ƙasa
- Hon. Babajimi Benson ya ce wajibi a kafa ‘yan sandan jihohi domin rage nauyin da ke kan sojoji da kuma inganta tsaro a matakin tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kwamitin Sojin ƙasa na Majalisar Wakilai ya bayyana damuwa bisa yadda ake yawaita daukar doka a hannu a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Wannan ya biyo bayan mummunan kisan da ake zargin 'yan banga sun jawo an yi wa fararen hula 16 a garin Uromi na jihar Edo, inda dukkan waɗanda aka kashe ‘yan Arewa ne.

Kara karanta wannan
'Dan sandan Najeriya ya rasu a gidan kallon ƙwallo ana wasan Arsenal da Real Madrid

Asali: Getty Images
Yayin hira da jaridar Punch, shugaban kwamitin, Hon. Babajimi Benson ya bayyana bukatar a sake duba tsarin tsaron cikin gida a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bukatar horas da 'yan banga a Najeriya
Benson ya ce mafi yawan 'yan banga a Najeriya ba sa aiki bisa horo ko tsari daga hukumomin tsaro na ƙasa, abin da ke barin ƙofa a bude ga cin zarafi da kashe-kashen da ba bisa ƙa’ida ba.
A cewarsa:
"Kisan fararen hula 16 a Edo babban lamari ne mai tayar da hankali. Wannan lamari ya nuna muhimmancin sauya tsarin tsaron cikin gida.
"Kafa ‘yan sandan jihohi ba batun siyasa ba ne— lamari ne da ya shafi tsaro."
Ya ce kafa rundunar ‘yan sanda a matakin jihohi za ta ba da dama a gudanar da tsaro yadda ya kamata, musamman ta fuskar gano bayanan sirri da fahimtar al’adun jama’a a matakin ƙasa.
'Akwai gyara a tsaron Najeriya' - 'Dan majalisa
Benson ya ce akwai matsala sosai a tsarin tsaron Najeriya, inda ya bayyana cewa adadin jami’an tsaron masu zaman kansu da hukumar NSCDC ta ba lasisi ya fi na sojoji da ‘yan sanda.
Ya bayyana hakan da cewa:
"Wannan rashin haɗin kai a tsarin tsaro babban gibi ne. Ba za mu iya ci gaba da barin tsaro ya zama a rabarrabe ba a ƙasa mai mutane fiye da miliyan 200 ba."

Asali: Facebook
Bukatar duba yanayin aikin soja a Najeriya
Dan majalisar ya ce ya kamata a mayar da rundunar sojin ƙasa kan aikin su na kare iyakoki, maimakon shiga harkokin tsaron cikin gida da ya kamata ya zama a hannun ‘yan sandan jihohi.
Ya jaddada cewa za a fi samun nasara wajen yaki da barayi, rikicin ƙabilanci da kuma matsalolin 'yan banga idan an samu tsaro da zai yi la'akari da yankuna da al’adunsu.
Me ke faruwa bayan kisan Hausawa a Edo?
A wani rahoton, kun ji cewa lauya mai kare hakkin dan Adam, Abba Hikima ya koka kan halin da ake ciki game da kisan Hausawa a Edo.
Barista Abba Hikima ya yi wasu tambayoyi guda 10 domin sanin halin da ake ciki yayin da aka doshi mako biyu da faruwar lamarin.
Haka zalika mutane da dama musamman a Arewacin Najeriya sun bukaci sanin halin da ake ciki game da matakin da aka ce za a dauka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng