An Shiga Alhini bayan Ɗan Majalisa Mai Ci a Zamfara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Shiga Alhini bayan Ɗan Majalisa Mai Ci a Zamfara Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Sanata Yau Sahabi ya nuna alhini kan rasuwar Aminu Ibrahim Kasuwar Daji, dan majalisar dokokin jihar Zamfara
  • Sahabi ya bayyana Aminu Kasuwar Daji a matsayin mutum mai biyayya da jajircewa wajen yi wa jama’arsa aiki da gaskiya da rikon amana
  • A cewar Sanata Sahabi, Aminu Kasuwar Daji mutum ne da tawali’u da gaskiya suka mamaye rayuwarsa, inda hakan ya zama abin koyi ga mutane
  • Sanatan ya yi addu’a Allah ya ji kansa da rahama, sannan ya bai wa iyalansa hakuri da juriyar rashin wannan babban mutum a rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Dan majalisar dattawa, Sanata Yau Sahabi ya yi alhinin rasuwar mamban majalisar jihar Zamfara.

Sanata Sahabi da ke wakiltar Zamfara ta Arewa, ya bayyana bakin ciki matuka kan rasuwar Aminu Ibrahim Kasuwar Daji.

Kara karanta wannan

Pascal Dozie: Abubuwa 11 da ya kamata ku sani game da attajirin da ya rasu a Najeriya

Sanata ya yi alhinin rasuwar dan majalisa a Zamfara
Sanata Yau Sahabi ya jajanta kan rasuwar dan majalisa a Zamfara, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji. Hoto: Abdulrazak Namadi Liman.
Asali: Facebook

Sanata ya jajanta rasuwar ɗan majalisar Zamfara

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa a bangaren sadarwa, Abdulrazak Namadi Liman ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin shi ke wakiltar mazabar Kaura Namoda ta Kudu a majalisar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.

Sanata Sahabi ya bayyana Aminu Kasuwar Daji a matsayin “bawan Allah mai biyayya,” wanda ya jajirce wajen yi wa al’ummarsa aiki da gaskiya da rikon amana.

Ya ce marigayin mutum ne mai saukin kai, gaskiya da kuma himma wajen aiki, abin da ya sa ya bar tarihi a jihar Zamfara.

Sanatan ya roki Allah Madaukakin Sarki ya jikan marigayin da rahama, ya kuma bai wa iyalansa da masoyansa hakurin jure rashinsa.

Zamfara ta yi rashin ɗan majalisa a jihar
An sanar da rasuwar ɗan majalisar jiha a Zamfara. Hoto: Legit.
Asali: Original

An sanar da lokacin sallar jana'izar ɗan majalisar

Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa za a sallar jana'izar marigayin a yau Laraba 9 ga watan Afrilun 2025.

Kara karanta wannan

Atiku da shugaban SDP sun ziyarci Aisha Buhari bayan an mata rashi

Rahoton ya ce za a gudanar da sallar da misalin karfe 3:00 na yammacin yau Laraba a garin Kasuwar Daji da ke karamar hukumar Kaura Namoda.

Marigayin, wanda aka fi sani da “Kasuwar Daji,” ya kasance ɗaya daga cikin fitattun ‘yan majalisar da ke taka rawa wajen kare muradun al’ummarsa a cikin zauren majalisa.

Mutane da ‘yan uwa da abokan aiki da kuma na arziki daga sassa daban-daban na ci gaba da isa Kasuwar Daji domin halartar jana’izar.

Rasuwar Hon. Aminu ta bar babban gibi a siyasar jihar Zamfara da kuma mazabarsa da yake wakilta, cewar Channels TV.

Al'umma da dama sun bayyana jimaminsu tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya gafarta masa, ya kuma bai wa iyalansa da abokan aikinsa haƙurin jure wannan rashi.

Tsohon dan majalisa a Najeriya ya rasu

A baya, mun ba ku labarin cewa mun samu labarin rasuwar tsohon shugaban masu rinjaye a Majalisar dokokin jihar Oyo, Hon. Kehinde Subair

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisa ya dura kan Tinubu da Shettima saboda ficewa Najeriya

Tsohon ɗan Majalisar Dokokin ya riga mu gidan gaskiya ne a Birtaniya ranar Juma'a, 13 ga watan Maris, mako guda kafin ya cika shekara 60.

Sanata mai wakiltar Oyo ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Yunus Akintunde ya yi alhinin rashin tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.