Bidiyoyin Shagalin Kamun Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Bidiyoyin Shagalin Kamun Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

  • Diyar Sanata mai wakiltan yankin Zamfara ta arewa, Sanata Sahabi Ya’u, za ta shiga daga ciki
  • Amina Sahabi za ta amarce da hadadden angonta mai suna Muhammad Auwal a karshen makon nan
  • An fara gudanar da shagalin bikin inda aka shirya wani kasaitaccen kamun amarya kuma tuni bidiyoyi da hotuna suka yadu a soshiyal midiya

Zamfara - Amina Kyakkyawar diyar sanata mai wakiltan yankin Zamfara ta arewa, Sanata Sahabi Ya’u, za ta shiga daga ciki.

Amina wacce ake kira da Ummi za ta auri angonta mai suna Muhammad Auwal a karshen wannan makon.

Amina da Auwal
Bidiyoyin Shagalin Taron Kamun Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi Hotto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Tuni shagalin bikin ya kankama domin an gudanar da wani kasaitaccen kamun amarya wanda ya kayatu matuka.

Shahararren mawakin nan na Arewa, Ali Isah Jita yana daga cikin mawakan da suka gabatar da wasa a wajen shagalin kamun.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda Aka Biya Dala 20,000 Kudin Kamun Diyar Sanata Sahabi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin bidiyoyi da hotunan shagalin da suka yadu a shafukan soshiyal midiya, an gano amarya cikin ado na kece raini, inda ta sanya doguwar riga da aka kawata da duwatsu masu ruwan gwal yayin da ango Auwal ya sha dinkin shadda babbar riga da hula zannan bukar.

Kalli bidiyoyin shagalin a kasa:

Ba’a Kyauta Mana Mu Talakawa: Rukayya Dawayya ta Koka Kan Yadda ‘Ya’yan Masu Kudi Ke Auran Junansu A Kasar

A wani labarin, Shahararriyar jarumar Kannywood, Rukayya Umar Dawayya ta yi martani a kan yadda ake yin kwarya tabi kwarya wajen kulla auratayya a kasar nan.

Dawayya ta shawarci ‘ya’yan talakawa da ke da kyau a kan su daina yarda da soyayya tsakaninsu da yaran masu kudi domin magana ta gaskiya ba auransu za su yi ba.

Kara karanta wannan

Hotuna da Bidiyon shagalin Kamun diyar Sanata Sahabi Yau sun Dauka Hankali

A cewarta koda yaran na son su iyayensu ba za su amince a kawo masu diyar talakawa a matsayin suruka ba, don haka ta shawarce su da su tashi su nemi ilimi don gobensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel