Farkon Damina: NiMet Ta Fadi Jihohi 12 da za a Sheka Ruwan Saman Kwanaki 3
- Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen saukar ruwan sama a wasu jihohi shida na Kudancin Najeriya, ciki har da Edo
- Daga ranar Laraba, 9 zuwa Juma'a, 11 ga watan Afilu, 2025, hukumar NiMet ta ce ana iya samun ambaliyar ruwa marar karfi a sassan kasar
- Za a fuskanci ruwa mai karfi gami da iska a Edo, Akwa Ibom da wasu jihohi hudu, amma za a samu yayyafi a Legas, Abia da wasu jihohin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen saukar ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu jihohin Najeriya daga Laraba zuwa Juma'a.
Hukumar ta yi hasashen samun ruwan sama marar karfi a wasu sassan kasar, yayin da ta ce akwai jihohin da ba za su samu ruwa a cikin kwanaki ukun ba.

Asali: Getty Images
NiMet: Hasashen ruwan sama na kwanaki 3
Daga ranar Laraba, 9 zuwa Juma'a, 11 ga watan Afrilun da muke ciki, hukumar NiMet ta ce za a zabga ruwan sama mai karfi a jihar Cross River, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran jihohin Kudu shida da NiMet ke hasashen ruwan sama zai sauka da karfi su ne: Akwa Ibom, Edo, Bayelsa Delta da Ogun.
Hukumar, a sanarwar hasashen yanayi da ta fitar a ranar Talata, ta kuma ce za a yi ruwan sama marar karfi a Ondo, Lagos, Delta, Imo, Abia sai Ekiti.
Sanarwar hukumar ta kara da cewa akwai wasu jihohin da za su fuskanci yayyafi, yayin da wasu jihohin ma ba za su samu ruwan sama ba a cikin kwanakin uku.
NiMet ta gargadi mutane kan tuki ana ruwa
Hukumar ta kuma bayyana cewa akwai yiwuwar aukuwar ambaliya sakamakon ruwan saman da zai sauka a sassan kasar nan.

Kara karanta wannan
"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi
NiMet ta jaddada cewa ana iya samun iska mai ƙarfi hade da ruwa, wanda ya sa take gargadin jama'a da kada su yi tukin mota yayin da ake ruwan sama domin kaucewa hadari.
Sauran shawarwarin da hukumar ta ba 'yan Najeriya sun haɗa da:
“Gujewa bin hanyoyi masu santsi, ruwa mai karfi da zai iya hana hangen nesa wanda zai iya hana zirga-zirga ko haddasa hadarin ababen hawa.
“Iska mai ƙarfi na iya rushe gine-ginen da ba su da ƙarfi, bishiyoyi da hasumiyoyi. A tabbatar an cire na'urorin lantarki kafin ruwan sama ya sauka, ba lokacin da yake sauka ba.”
Matakai 7 da ya kamata mutane su dauka

Asali: Getty Images
A wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X, NiMet ta ba 'yan Najeriya shawarar abin da ya kamata su yi a ranar Laraba, 9 ga Afrilu:
- Zafin rana mai tsanani na iya haddasa gajiya – a sa kaya masu laushi kuma a zauna a wuri mai sanyi.
- A rika shan ruwa da yawa don hana bushewar jiki.
- A guji fitowa cikin rana daga ƙarfe 12:00 na rana zuwa 3:00 na yamma.
- A kauce wa cunkoso, musamman a Arewacin ƙasar – a kula da tsaftar jiki da muhalli.
- Ruwan sama mai karfi na iya sauka da iska – a ɗauki matakan kariya.
- A bi duk shawarwarin tsaro daga hukumomi.
- A ci gaba da samun bayanai daga hasashen yanayi na NiMet a shafin: www.nimet.gov.ng
Ruwan sama ya lalata gidaje a Kebbi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ruwan sama mai haɗe da iska ya lalata sama da gidaje 100 a cikin jihar Kebbi a daminar 2023.
Sakataren gwamnatin Kebbi, Alhaji Yakubu Bala, ne ya bayyana wannan lokacin da yake jajantawa waɗanda abin ya shafa.
Gwamnatin jihar Kebbi, karkashin jagorancin Dakta Nasir Idris, ta yi alkawarin tallafawa dukkan waɗanda iftila'in ruwan ya shafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng