Gwamnatin Tinubu Ta Dauki Babban Mataki da Amurka Ta Kakaba Haraji kan Najeriya
- Gwamnatin tarayya na ƙoƙarin ƙarfafa samun kuɗaɗe daga sassa daban-daban domin rage illar harajin da Amurka ta kakabawa Najeriya
- Ministan kudi ya ce kwamitin tattalin arziki zai nazarci harajin kaso 14% da Amurka ta sanya, tare da gabatar da matakan rage illarsa
- Najeriya ta fitar da kayayyaki na N5.5tr zuwa Amurka a 2024, inda kashi 92% suka kasance daga mai da ma'adinai, in ji ministan, Wale Edun
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ministan Kuɗi, Wale Edun, ya ce gwamnatin tarayya za ta ƙarfafa samun kuɗaɗen shiga ba ta hanyar dogaro da mai ba.
Wannan mataki na daga cikin hanyoyin da gwamnatin ke kokarin bi domin rage illar harajin kayayyaki da Amurka ta sanya wa ƙasashen duniya.

Asali: Getty Images
Najeriya za ta yi nazarin harajin Amurka
Channels TV ta rahoto Wale Edun ya ce kwamitin kula da tattalin arziki zai zauna domin nazarin tasirin harajin kashi 14% da Amurka ta saka kan fitar da kaya daga Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce bayan ya gudanar da zaman, kwamitin zai gabatar da shawarwari domin rage illar da hakan zai iya yi wa tattalin arzikin ƙasar.
Mista Wale Edun ya bayyana haka ne a wani taro da ma’aikatar kuɗi (MOFI) ta shirya a ranar Litinin a Abuja, inda ya ce illar harajin zai shafi Najeriya ta fuskar faduwar farashin danyen mai.
Ya kara da cewa gwamnati na ƙara ƙaimi wajen ƙara yawan hakar danyen mai da kuma samun kuɗin shiga daga fannonin da ba na man ba.
Bayanin harajin da Amurka ta kakaba wa Najeriya
Mun ruwaito cewa, gwamnatin Donald Trump ta sanya haraji daga kashi 10% zuwa 65% kan kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashe daban-daban.
Najeriya kuwa ta samu harajin kashi 14% kan kayayyakin da take fitarwa zuwa Amurka, inji rahoton ThisDay.
Sai dai ministan kudin ya bayyana cewa Amurka ta sanar da cire haraji daga ma’adanai, ciki har da danyen mai, daga ranar 2 ga Afrilu.
Saboda haka, Wale Edun ya shaida cewa abin da zai iya shafar Najeriya shi ne canjin farashin danyen mai a kasuwa.
Ya ce kwamitin tattalin arzikin shugaban kasa Tinubu yana da alhakin duba yuwuwar sauye-sauye da shirin da ya dace don dakile illar harajin.
Najeriya za ta samar da hanyoyin samun kudi

Asali: Facebook
A jawabin da ya fara gabatarwa a taron, ministan ya ce gwamnati na duba yiwuwar sake fasalin kasafin kuɗi da fifita muhimman ayyuka.
Ya kuma shaida gwamnati na kokarin samar da hanyoyin samun kuɗi ba tare da ta dogara da karbo rance daga ciki ko wajen kasar ba.
A cewarsa, Najeriya ta fitar da kaya na N1.8tr a 2022, N2.6tr a 2023 da N5.5tr a 2024, wanda ya sa ta zama a sahun gaba na masu shigar da kaya Amurka.
Ya bayyana cewa kashi 92% na kayan da ake fitarwa sun danganci mai da ma’adinai, wanda ya kai N5.08tr, yayin da sauran kayan da ba na man fetur ba suka kai kimar N0.44tr kacal.
Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamitin kasashen waje na majalisar wakilan Amurka ya amince wa Shugaba Donald Trump ya kakaba wa Najeriya takunkumi.
Wannan mataki ya biyo bayan zaman jin bahasi, inda aka zargi Najeriya da kasa kare Kiristoci daga hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai musu.
Rahoton ya nuna cewa daga Oktoba 2019 zuwa Satumba 2023, an kashe mutane 55,910, yayin da ‘yan ta’adda suka sace kimanin 21,000 a Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng